ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, June 24, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Na Ɗauki Harkar Fim Tamkar Aikin Gwamnati — Maryam Usman

by Rabi'at Sidi Bala
6 months ago
Fim

Shafi ne da ya saba zakulo muku fitattun jarumai manya da kanana daga cikin masana’antar shirya finafinan hausa ta Kannywood, kamar kowane mako yau ma shafin na tafe da wata fitacciyar jarumar wacce ta shafe tsahon shekaru a cikin masana’antar Kannywood wato, HAJ. MARYAM USMAN wacce aka fi sani da ANTI MA Inda ta bayyana wa masu karatu irin matsalolin da ake fuskanta a cikin masana’antar Kannywood, kana Jarumar ta yi bayani game da abin da ya shafi rayuwarta da kuma sana’ar ta. Baya ga haka jarumar ta bayar da shawarwari ga masu kokarin shiga harkar fim, har ma da wasu batutuwan masu yawa.

Ga dai tattaunawar tare da wakiliyar jaridar LEADERSHIP HAUSA RABI’AT SIDI BALA Kamar haka:

Da farko za ki fadawa masu karatu cikakken sunanki tare da sunan da aka fi saninki da shi.

ADVERTISEMENT

Sunana Haj. Maryam Usman Na’ibawa, wacce aka fi sani da ‘Aunty Ma’.

  • Tun Ina Yarinya Sana’ar Fim Ke Burge Ni —Hafsat Salisu
  • Babbar Kasuwar Fim Ta Sin Babbar Damar Nollywood Ce

Ko za ki fadawa masu karatu dan takaitaccen tarihinki?

LABARAI MASU NASABA

Zan Iya Auren Namiji Komai Talaucinsa Muddin Muna Son Junanmu -Maryam Labarina

Gidajen Gala Ne Kadai Mafita Ga Masana’antar Kannywood – Falalu Dorayi

An haife ni a garin Kano, amma asalina ‘yar Adamawa ce, kuma asalina ‘yar Maiduguri ce, sannan kuma yaren Margi ce ni. Bayan na girma a Kano na fara karatu a makarantar sojoji ‘Bokabo Barrack’, daga nan muka bar ‘Katsina Road’ muka koma ‘Yar Akuwa. Na fara firamare ‘Gidan Gona Special Primary School’. Bayan nan na tafi ‘Jigawa state’ wato Malam Madori, a ‘first time’ ‘yar’uwata ta rasu. Aka canja min makaranta aka dawo da ni ‘Gobernment Secondary School Kura’, a nan na kammala aji shida. Daga nan na tafi ‘Federal Polytechnic Yola’ a nan na karasa karatuna wanda nake da diploma. A yanzu kuma ina Na’ibawa a nan na girma, a nan aka yi min aure, yanzu komai nawa da Na’ibawa nake ‘bearing’.

 

Wane rawa ki ke takawa a cikin masana’antar Kannywood?

Ina taka rawa matsayin jaruma, kuma ina fitowa a matsayin mahaifiya me fadakarwa a cikin Kannywood, duk fim din da za a yi a uwa nake fitowa ba a taba canja min rol ba, kuma na san ba za a taba canja min rol din ba. Saboda ina aktin din iyaye, abin da iyaye suke yi shi nake yi. Shi ya sa a kowane fim za ki ga ana sha’awar saka ni na fito a uwa.

 

Me ya ja hankalinki har ki ka tsunduma cikin masana’antar Kannywood?

Ni dai na san abu ne me kyau, sannan kuma fadakarwa ne. Tun ina sakandare nake yin harkar fim. Babban abin da ya ja hankali na fadakarwar da fim yake, in kana son sako ya isa a minti daya to, harkar fim ita kadai za ta iya wannan abun,

 

Za ki yi kamar shekara nawa da fara fim?

Bayan na fito daga gidan mijina na dan kwan biyu ina wasu ‘business’ dina na harkar abinci, sai kuma na zo na shiga fim. Ban fi shekara biyu ba sai na yi aure, bayan na yi auren kuma da wasu shekaru sai na dada fitowa. Amma daga farawata zuwa yanzu zan yi shekara goma zuwa sha daya da harkar fim.

 

Ya gwagwarmayar shiga cikin masana’antar ta kasance?

Ni ban sha wata gwagwarmaya ba, saboda Sadik N-Mafia shi ya kai ni fim. Da akwai wata mawakiyar Sadi Sidi Sharifai wato Ummi Nagarta, ‘yar’uwa take a guna. Lokacin muna harkar siyasa an ba ni ‘women leader’ na ce mata ina son fim. Lokacin ina ta tunanin ina zan samu Sadik N-Mafia, ta ce to, tunda dan’uwanta ne na zo ta kai ni wajensa. Muna zuwa wajensa washegari na siyi ‘form’, wata washegarin aka fara fim da ni wani fim wai shi ‘Magana Jari’, aka ba ni wani rol me karfi, ban sha wahala ba. Da yake mu fim din kamar a jinin mu yake, ina da ‘yan’uwa da yawa a cikin Kannywood din nan, akwai; Halima Atete, Teemah Makamashi, Isma’il Fish, Aisha Humairan Rarara wacce ‘ya ce a guna uwarta aminiyata ce, sannan akwai Bana, sannan Stephening ta Arewa24 ‘yar’uwata ce to, kin ga mu mun mayar da fim sana’a.

 

Ya batun iyaye lokacin da za ki sanar musu kina sha’awar fara fim, shin kin samu wani kalubale daga gare su ko kuwa?

Gaskiya ban samu wata matsala ba, saboda akwai kanwata ana ce mata Sadiya ta rasu ita ta fara yin fim a gidanmu, har su Atete duk a bayanta suka yi fim. Sannan kuma mahaifiyata da mahaifina wayayyu ne duk abin da yaro yake so, indai ba na batanci bane suna so. Ko lokacin da na shiga fim mahaifina ya rasu sai mahaifiyata, zan iya lissafo miki manyan Kannywood wadanda suka san mahaifiyata wacce suka zo gabanta suka yi mata bayani ta ba ni ‘direct ticket’ ta ce na je, kuma a gabansu ta saka min albarka kuma har yau albarkar ce take dawainiya da ni.

 

A baya kin yi maganar kin fara fim me suna Magana Jari, ya karbuwar fim din ya kasance ga su masu kallon a lokacin?

Eh, na fara da Magana Jari, za ki ga ana yawan nuna shi a DSTB, sannan na zo na yi wani fim Sarka, lokacin ban waye ba sosai. Jamila Nagudu ce ta zaunar da ni ta ce in daina tsoron ‘Camera’, na tsaya na bude idona nayi abu me kyau, shi ma fim din ya karbu. Sannan na zo nayi Ibro Me Kilago, shi ma ya karbu sosai. Sannan a yanzu duk wani fim da ake yi a duniya indai aka saka ni za ki ga fim din ya fashe sosai, saboda wannan tijarar da nake yi.

 

Ya farkon farawar ya kasance?

Za ki ji na ce na tsoraci ‘camera’ Jamila ta gyara min, wannan shi ne na uku. Haske ne ya sa na tsoraci ‘Camera’, amma ko ranar da aka fara dora min ‘canera’ tambayata aka yi ta yi “daman kin saba yin fim?” na ce wannan ne na farko. Amma abin da ya sa ya yi kyau, wannan addu’ar mahaifiyar tawa ce. A fim dina na farko shi ne na hadu da Adaman Kamaye, ba na mantawa mun yi wasu finafinai muka fada tarkon ‘yan sanda ta dauko ni a motarta, muka dawo gida. Wannan shI ne dawowata na biyu kuma sai na dawo da daukaka da albarka.

 

Kin yi finafinai sun kai kamar guda nawa?

Wai! ai finafinan da na yi sun fi dari, bana iya kirga su, saboda ni a wata zan iya yin fim ashirin.

 

Ko za ki iya lissafowa masu karatu kadan daga ciki?

Akwai; Lulu da Andalu na darakta Dan Hausa, Mashahuri na Yakubu Muhammad, Mage da Wuri na Hussaini Bacci, Manyan Mata na Abdul Amart, So Ne na Sultan, Garwashi na Uk, Lokaci na Tijjani Asase. To, suna da yawa gaskiya.

 

Cikin finafinan da ki ka fito, wane fim ne ya zamo bakandamiyyar ki?

Kowane fim bakandamiyata ce, ko ‘comedy’ na yi sai ya zama bakandamiyata.

 

Ko akwai wani kalubale da ki ka taba fuskanta tun daga farkon shigarki masana’antar, zuwa yanzu?

Kalubalen da na fuskanta wata mata ce wacce ta tsaya tana ta tsine min a kan an saka ni a fim din Garwashi, ta ce na takurawa ‘ya ta. Amma na ga tsohuwa ce bata fuskanci mene ne fim ba, shi kadai ne kalubale na. Kuma ban ji haushi ba, da yake sana’a ta ce, ita bata san mene ne fim ba.

 

Wadanne irin nasarori ki ka samu game da fim?

A cikin wannan masana’antar ta Kannywood na samu wata daukaka ta zama ‘Women leader’ a kungiyar Adon Garin Kasar Hausa, ta rantsar da ni a matsayin shugabar mata a Jihar Kano ranar litinin. Da na a makaranta ya samu babban mukami a dalilin uwarsa ‘yar fim ce, sannan ‘ya ta, ta sami babban mukami a dalilin uwarta ‘yar fim ce. Kuma lokacin da aka tura min ita garin iyamurai aka ce ta je bautar kasa, da na je a take babu abin da na kashe aka ba ni inda nake so wato Maiduguri garinmu. Sannan kuma na samu kyaututtuka da dama wanda ba sai na bayyana ba, to, kin ga ni ba zan iya barin fim ba. Na samu abubuwa da yawa kudade, kayan sakawa, alfarma a asibiti, ‘yan’uwana sun sassami alfarma da yawa a dalilina. Kuma ‘yan’uwana da yawa suna aikin gwamnati a dalilin harkar fim na sassamu alfarma da yawa.

 

Ya ki ka dauki fim a wajenki?

Na dauki fim babbar sana’a, saboda yadda dan gwamnati yake jin kansa a aikin gwamnati, haka nake jin kaina a aikin fim. Yadda dan majalisa yake jin kansa a ofis, haka nake jin kaina. Kuma yadda shugaban kasa yake jin kansa yana da mulki a karkashin ikonsa, haka nake jin dadi ina fim ina fadakar da mutane,

shi ne sana’a ta.

Za mu ci gaba a makon gobe

Fim
Rabi'at Sidi Bala
+ postsBio
  • Rabi'at Sidi Bala
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiat-sidi-bala/
    Zan Iya Auren Namiji Komai Talaucinsa Muddin Muna Son Junanmu -Maryam Labarina
  • Rabi'at Sidi Bala
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiat-sidi-bala/
    Gidajen Gala Ne Kadai Mafita Ga Masana’antar Kannywood – Falalu Dorayi
  • Rabi'at Sidi Bala
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiat-sidi-bala/
    Bukatar Rike Sirri A Tsakanin Ma’aurata
  • Rabi'at Sidi Bala
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiat-sidi-bala/
    GORON JUMA’A

MASU ALAKA

Zan Iya Auren Namiji Komai Talaucinsa Muddin Muna Son Junanmu -Maryam Labarina
Nishadi

Zan Iya Auren Namiji Komai Talaucinsa Muddin Muna Son Junanmu -Maryam Labarina

June 14, 2026
Gidajen Gala Ne Kadai Mafita Ga Masana’antar Kannywood – Falalu Dorayi
Nishadi

Gidajen Gala Ne Kadai Mafita Ga Masana’antar Kannywood – Falalu Dorayi

June 14, 2026
Ban Taɓa Fitowa A Fim Na Yi Da-na-sani Ba —Habibu Yaro
Nishadi

Ban Taɓa Fitowa A Fim Na Yi Da-na-sani Ba —Habibu Yaro

May 31, 2026
Next Post
Yadda Ake Yin Pizza A Gida

Yadda Ake Yin Pizza A Gida

LABARAI MASU NASABA

Tinubu Ya Gaza Wajen Magance Matsalar Tsaro A Nijeriya — Atiku

Atiku Ya Soki Tsare El-Rufai, Ya Ce Sharuɗan Belinsa Sun Yi Tsauri

June 24, 2026
Trump Ne Zai Jagoranci Bayar Da Kofin Duniya A Wasan Ƙarshe – Infantino

Trump Ne Zai Jagoranci Bayar Da Kofin Duniya A Wasan Ƙarshe – Infantino

June 24, 2026
‘Yansanda Sun Kama Ɗan Bindiga Da Kuɗin Fansa Naira Miliyan 5 A Delta

’Yansanda Sun Kama Wani Mutum da Harsasai 174 A Nasarawa

June 24, 2026
Sojoji Sun Kama Ɗan Fashi Da Makami A Taraba

Sojoji Sun Kama Ɗan Fashi Da Makami A Taraba

June 24, 2026
An Kashe Mutum 2, 8 Sun Jikkata Yayin Rikici A Bauchi

An Kashe Mutum 2, 8 Sun Jikkata Yayin Rikici A Bauchi

June 24, 2026
Tsohon Shugaban APC Na Kebbi Ya Rasu A Hannun ’Yan Bindiga

Tsohon Shugaban APC Na Kebbi Ya Rasu A Hannun ’Yan Bindiga

June 24, 2026
Ya Kamata Sin Da Birtaniya Su Yi Aiki Tare Don Ci Gaba Da Inganta Dangantakarsu

Ya Kamata Sin Da Birtaniya Su Yi Aiki Tare Don Ci Gaba Da Inganta Dangantakarsu

June 23, 2026
Firaministan Sin Ya Jaddada Muhimmancin Kara Azamar Bunkasa Kirar Kayayyakin Aikin Masana’antu Na Zamani

Firaministan Sin Ya Jaddada Muhimmancin Kara Azamar Bunkasa Kirar Kayayyakin Aikin Masana’antu Na Zamani

June 23, 2026
Gombe Ta Zabge Farashin Taki Da Kashi 50 Cikin 100

Gombe Ta Zabge Farashin Taki Da Kashi 50 Cikin 100

June 23, 2026
Wang Yi Ya Gana Da Babban Sakataren Majalisar Tsaron Masar Da Ministan Fadar Gwamnatin Afirka Ta Kudu A Indiya

Wang Yi Ya Gana Da Babban Sakataren Majalisar Tsaron Masar Da Ministan Fadar Gwamnatin Afirka Ta Kudu A Indiya

June 23, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.