Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), ta bayar da bayani kan yadda ta ki fitar da sunayen ainihin wadanda suka lashe zaben ‘yan takarar sanata na jam’iyyar APC mai mulki a matakai guda biyu.
A cikin wani yanayi mai cike da cece-kuce, an rasa sunayen shugaban majalisar dattawa, Sanata Ahmad Lawan, tsohon ministan harkokin Neja Delta, Godswill Akpabio.
- Mutane 880 Sun Kamu Da Korona A Ranar Asabar – NCDC
- Kasar Sin Ta Yi Kira Da A Warware Sabanin Siyasa A Yammacin Afirka Da Sahel Ta Hanyar Shawarwari
Bashir Machina da Udom Ekpoudom sun fito zaben fidda-gwani na sanata a Yobe ta Arewa da Akwa-Ibom ta Arewa maso Yamma wanda INEC ta shaida, sai dai sunayen Lawan da Akpabio APC ta mika wa hukumar.
Dangane da rade-radin nuna son kai da wani bangare na al’umma ke yi wa INEC, hukumar a wata sanarwa da ta fitar a ranar Asabar, ta ce an tafka kura-kurai a kan matakin da ta dauka.
Dangane da mazabun biyu, hukumar ta ce ta sauke ayyukan da kundin tsarin mulkin kasar ya ba ta na sanya ido kan harkokin kudaden jam’iyyun siyasa da zabukan fidda-gwani.
Hukumar ta INEC ta tsaya tsayin daka wajen amincewa da rahotannin ofisoshinta na jihohi dangane da zaben ‘yan majalisar dattawa na jam’iyyar APC a yankunan da abin ya shafa tare da kalubalantar mambobin da suka koka da su garzaya kotu.
“Dangane da zabukan fidda-gwani na ‘yan majalisar dattawan Akwa Ibom ta Arewa maso Yamma da Yobe ta Arewa, hukumar ta tsaya kan rahoton sa ido da aka samu daga ofisoshinmu na jiha.
“Saboda haka, hukumar ba ta buga bayanan kowane dan takarar mazabar biyu ba sabanin rahoton jihar ba.
“A yanzu haka, hukumar ta na aiki tukuru a kan matsalolin biyu. Masu korafin suna da ‘yancin tunkarar babbar kotun tarayya domin neman hakkinsu kamar yadda sashe na 285 na kundin tsarin mulkin tarayyar Nijeriya 1999 da sashe na 29(5) da 84(14) na dokar zabe. 2022, ” in ji Festus Okoye.
Machina da Ekpoudom sun samu shiga rahoton ofisoshin jihohin Yobe da Akwa-Ibom na hukumar a lokacin da Lawan da Akpabio sun zage damtse wajen samun damar lashe tikitin takarar shugaban kasa na APC.
Yayin da Mista Akpabio ya janye takarar neman takarar shugaban kasa, Bola Tinubu, Mista Lawan ya sha kaye a hannun tsohon gwamnan na jihar Legas.
Ganin yadda ake ta cece-kuce a kan takardun da aka buga na wasu daga cikin ‘yan takarar shugaban kasa da na ‘yan majalisun tarayya da na gwamnoni, INEC ta ki buga sunayen ‘yan takarkarun da ake da matsala a yankunansu.