Shugaban Majalisar Wakilai, Abbas Tajudeen, ya nuna fargaba kan yadda Nijeriya ke ci gaba da amso basussuka, yana mai gargadin cewa hakan, ya keta ƙa’idojin da aka shimfida a ƙasar, wanda hakan ke zama babbar barazana ga tattalin arzikin ƙasar.
Da yake magana a ranar Litinin a wurin bude taron shekara-shekara karo na 11 na babban taron kungiyar kwamitocin asusun jama’ar Afirka ta Yamma (WAAPAC) a Majalisar Dokoki ta kasa, Abuja, Abbas ya ce bashin Nijeriya ya kai “kololuwar matsayi mai razanarwa” kuma ya yi kira da a yi sauye-sauye cikin gaggawa kan tsarin karbar lamuni.
“Ya zuwa rubu’in farko na shekarar 2025, jimillar bashin da ake bin Nijeriya ya kai Naira Tiriliyan 149.39, kwatankwacin dalar Amurka biliyan 97. Wannan ya nuna yadda adadin ya yi tashin gwauron zabi daga Naira Tiriliyan 121.7 a shekarar da ta gabata.”
Ya bayyana karya ka’idojin da aka shimfiɗa kan amso basussukan a matsayin “babban abin damuwa da fargaba kan ɗorewar tattalin arzikin kasar,” yana mai jaddada cewa, akwai buƙatar samar da “sabbin tsaruka masu ƙarfi, da za su daidaita hanyoyin karɓar rance na gaskiya, da kuma ƙuduri na bai ɗaya don tabbatar da cewa, duk kuɗin da aka karɓo ya dace da buƙatar shirin inganta zamantakewar ‘yar Nijeriya”.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp