Kwararren koci dan Faransa kuma tsohon dan wasa Zinedine Zidane, ya bayyana dalilin da ya sa bai zama kocin Manchester United ba a lokacin da suke da bukatar mai koyarwa.
A wata hira da ya yi da L’Equipe, Zidane ya ce bambancin yare ya hana shi zama dan takara mai neman kocin kungiyar Man U dake buga gasar firimiya.
Ya ce, “Idan na koma kulob, tsari Na shi ne, na yi nasara. Ina fadin haka cikin kankan da kai. Shi ya sa ba zan iya zuwa ko wane irin Kulob ba.
“Lokacin da mutane suke yawan tambaya ta: ‘Shin me yasa ba za kaje Manchester ba?’ Na ce musu, Ina fahimtar Turanci amma ban kware sosai ba.
“Na san cewa akwai masu koyarwa da yawa da suke zuwa kulob ba tare da jin yaren Kasar ba, amma ni tsari na daban yake da na kowa. In ana son samun nasara, akwai abubuwa da ake bukata da yawa don cin ma nasara. Ni, na san abin da nake bukata don yin nasara.”