An bayyana dan takarar Jam’iyyar APC, Mista Biodun Oyebanji, a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan Ekiti da aka yi a ranar Asabar.
Da yake bayyana wanda ya lashe zaben, Farfesa Oyebode Adebowale, jami’in hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC), ya ce Oyebanji ya lashe zaben ne da kuri’u 187,057.
Ga abubuwa biyar da jaridar Daily trust ta tatso game da zababben gwamnan.
- Haihuwa
Biodun Abayomi Oyebanji, wanda aka fi sani da BAO, dan siyasa ne kuma dan jam’iyya APC, wanda aka haifa a ranar 21 ga Disamba, 1967 a Ikogosi-Ekiti, jihar Ekiti. Yana da shekaru 54.
- Ilimi
Ya yi digirin farko na Kimiyya (BSc) a fannin Kimiyyar Siyasa a Jami’ar Jihar Ondo (Jami’ar Jihar Ekiti, Ado-Ekiti a yanzu) a shekarar 1989 sannan kuma ya ci gaba da karatunsa a Jami’ar Ibadan ta Jihar Oyo a 1992 inda ya samu Digirinsa na biyu (M.Sc) a Kimiyyar Siyasa (Bangaren zumuncin kasa-da-kasa da Tsare-tsare a tsakaninsu)
- Tsohon malamin Jami’a ne
Oyebanji ya fara aiki a matsayin malami a Sashen nazarin kimiyyar siyasa na Jami’ar Ado Ekiti, inda ya karantar na tsawon shekaru hudu (1993 – 1997) daga baya ya koma aikin banki a rusasshiyar bankin Omega. Plc (yanzu Bankin Heritage) har zuwa Mayu 1999.
- Tsohon Sakataren gwamnatin Jihar Ekiti
Har sai da ya yanke shawarar tsayawa takarar gwamnan Ekiti, Oyebanji ya kasance sakataren gwamnatin jihar Ekiti a karkashin Gwamna mai ci Kayode Fayemi.
- Iyali
Yana aure da Misis Oyebanji, wata gimbiya a masarautar Ado Ekiti kuma farfesa a jami’ar Ibadan.