Shugaban kasa Bola Tinubu, ya nada Ola Olukoyede, a matsayin sabon shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa da yi wa tattalin arziki zagon kasa.Â
Kazalika, Majalisar Dattawa ce ta tabbatar da nadin Olukoyede, a matsayin sabon shugaban na EFCC.
- Tinubu Ya Nada Olukoyede A Matsayin Sabon Shugaban EFCC
- Gwamnatin Bauchi Ta Kori Shugaban Kungiyar Kwallon Kafa Ta Wikki Tourist
An nada Olukoyede a mukamin ne, bayan an dakatar tare da tsige tsohon shubaban hukumar Abdulrasheed Bawa, ‘yan watanni da suka wuce bisa zarginsa da saba ka’idar aiki.
Bugu da kari, kafin wannan sabon nadin na Olukoyede, ya yi aiki a bayan fage a shekaru da dama a EFCC.
Ga wasu abubuwa biyar da ya kamata ku sani game da sabon shugaban EFCC.
1. Olukoyede, shi ne na farko da ya fito daga jihar Ekiti da ke a kudancin Nijeriya da aka taba nada wa shugaban hukumar na farko, tun a lokacin da aka kafa hukumar.
2. Shi kwararren lauya ne wanda ya shafe sama da shekaru yana yin aiki, a matsayin lauyan tuntuba wanda kuma ya kware a fannin binciken aikata badakala da sanin bayanan sirri.
3. Kazalika, Olukoyede yana da cikakkiyar kwarewa akan gudanar da ayyukan EFCC ganin cewa, a lokuta daban-daban ya taba rike mukamin shugaban ma’aikata a lokacin shugabancin mukaddashin riko na EFCC Ibrahim Magu, daga 2016 zuwa 2018, ya kuma rike mukamin sakatare na EFCC daga 2018 zuwa 2023.
4. Bugu da kari, sabon shugaban ya samu shaidar kammala karatun jami’ar jihar Legas, ya kuma samu shaidar kammala karatu a cibiyar ICC da ke Faransa, ya samu wata takardar kammala karatu a jami’ar Harvard ya kuma kara samun wata takardar kammala karatu a makarantar Kennedy.
5. Ola Olukoyede, Fasto ne kuma limami a Cocin Redeemed (RCCG).