Rayuwar aure an gina ta ne kan nutsuwa da soyayya da tausayi, tsakanin miji da matarsa, tare da fahimtar juna da girmama juna ko mutuntawa da kyakkyawan zama a tsakanin miji da mata ta yadda za su yi rayuwa mai tsawo, ba tare da wani ya shiga hakkin wani ba.
Wannan ya sa shaidan yake kai kawo da zirga zirga da kulle-kulle da kutunguila wajen lalata harkar aure, saboda ya san in aure ya lalace komai zai iya lalacewa sakamakon lalacewar sa. Wannan ya sa Malamai da masu ba da tarbiyya da kuma masu lura da al’amuran al-umma suke kara wayar wa da alumma kai, akan sake-saken sure da kuma hadarinsa wanda sakamakon ya kan haifar da rugujewar gida, tabarbarewar tarbiyya da lalacewar tsaro da rashin zaman lafiyar al-umma. Don haka muka yi nazari bayan bincike da tattaunawa, da wadanda suka shiga irin wadannan matsaloli.
- Mataimakin Firaministan Kasar Sin Ya Gana Da Tawagar Amurka Ta Rukunin Ayyukan Hada-hadar Kudi Na Sin Da AmurkaÂ
- Gobara Ta Kone Shagunan Hatsi 19 A Adamawa
Don haka muka fitar da dalilai guda sittin 61 wadanda muke ganin su ne Ummul Haba’ isin wadannan matsaloli wadanda idan ba a kula da suba za a samu mutuwar aure.
Mun kasa wadannan matsaloli zuwa kashi uku 3 : Na daya. Matsalolin da suke faruwa kafin aure. Na biyu, matsalolin da suke faruwa lokacin aure. 3. Matsalolin da ke faruwa bayan aure.
Wadannan matsaloli guda uku a kwai masu zuwa daga bangaren mata, akwai masu zuwa daga bangaren maza, akwai masu zuwa daga duka bangarorin guda biyu.
Don haka cibiya mai Suna “Lobe And Mercy School For Marriage Counseling”
ta dauki wadannan abubuwa daya bayan daya take shirya bitoci a kai.
Al-adu, Rashin Ilimin zamantakewar aure, rashin zabo matar kirki tagari, Auren da babu soyayya daga miji ko mata. Gaggawar yin aure ba tare da mutum ya shirya ba.
Banbancin Ilimi, Rashin binciken halin miji kafin aure. Rashin binciken halin mata kafin aure, Matsalar iyayen miji, Matsalar iyayen mata, Matsalar dangin miji, Matsalar dangin matar. Rashin tsafta. Rashin iya kwalliya, Rashin iya magana, Rashin ciyarwa, Rashin iya kwanciyar aure, Rashin adalci, Goyon kaka (Yar Shagwaba), Auren kisan wuta, Zaman gidan haya, Ruwan ido wajen neman aure, Auren bariki, Auren mace don kudinta ko danginta, Auren dole, Matsalar talauci.
Matsalar kawaye, Zafin kishi, Rashin haihuwa, Rashin ladabi, Rashin kunya, Shaye-shayen kayan maye, Kannen miji, Kannen amarya, Abokan miji, Sata, Gulma, tsananin damuwa, Rashi lafiyar mace wajen gamsar da miji, Rashin lafiyar miji wajen gamsar da matarshi, Sharrin bokaye. Rashin shawara tsakanin miji da mata, Aikin mace (Ta zama yar kasuwa ko ma’aikaciya, Rashin Ilimi da Samun wayewa akan aure, Rashin daukar nauyin iyali wajen basu hakki.
Cin bashi a yi aure, Yawan tafiye-tafiye (Bala Guro), Yawan zuwa unguwa, Cin amanar aure daga miji ko mata, Shigar da kawaye ko abokai cikin harkar iyali, Rashin kula da addini. Girman kan daya daga cikin ma’aurata.
Rashin daukar aure a matsayin Ibada, Butulci da manta alheri, Samun larura ko wani ciwo mai tsanani, Yawan shigar iyaye cikin harkar aure, Al’mubazzaranci, Rashin godiya, Mummunan zato, da kuma Rashin nuna tausayi da damuwa da juna.
Allah ya daidaita tsakanin ma’aurata ya ba da zaman lafiyar aure, Amin.