Bishiyar Kanya, wadda a turance ake kiran ta da ‘Black Ebony’, na kammala girma ne bayan ta gama rika.
Haka zalika, ta na iya shafe shekara dari ba tare da wani abu ya same ta ba, sannan tana iya yin tsawon da ya kai akalla kafa 50.
- An Tarwatsa Masu Zanga-zanga Kan Kokarin Kunna Wuta A Kofar Gidan Gwamnatin Kano
- An Tarwatsa Masu Zanga-zanga Kan Kokarin Kunna Wuta A Kofar Gidan Gwamnatin Kano
Har ila yau, ba sai ta kai tsawon wadannan shekaru 50 ko 100 ake iya fara cin moriyarta ba.
Bishiyar na daya daga cikin bishiyoyi masu tsada a fadin duniya, sannan akasarin mutane, ba su san muhimmancin da bishiyar take da shi ba, haka nan a jikinta ne ake samar da Gawayin Kwal tare da kuma sarrafa bishiyar wajen yin kujeru, gado da sauran makamantansu.
Wasu muhimman abubuwa guda shida ya kamata a sani da bishiyar ta Kanyar su ne: Bishiyar na yin tsawon da ya kai kafa 50, sannan kuma ta fi kowace bishiya tsada a duniya.
Sauran muhimman abubuwan sun hada da; ba a cika samun bishiyar a fadin duniya ba, kazalika kuma tana girma ne a hankali a hankali.
Haka nan, bishiyar na yin rassa masu yawan gaske, kana nauyinta kuma ya kai daga kilo 30 zuwa 68, shi yasa farashinta ke da matukar tsada.
Dabbobi kamar su Birai, Giwa, Jimina, Karkanda da sauransu; na dogara ne kan Bishiyar wajen samun abincin da za su ci, ana kuma yin amfani da Ganyenta wajen yin maganin zazzabin cizon Sauro ko kuma maganin Tari.
Tarihin Bishiyar Kanya:
Tarihinta ya samo asali ne daga wasu kasashe da suka yi fice a duniya wajen samun kyakkyawan dausayi, inda hakan ya sa ake iya shuka ta har ta kai munzalin zama babbar bishiya; wadda za a iya yin hada-hadar kasuwancinta a dukkanin fadin duniya.
Yanzu haka, farashin ingantacciyar bishiyar na kai wa dala 8,500 kowace mita daya, haka nan sarrafa Tumbarta daya zuwa wasu kayan kade-kade na zamani na kai wa dala 12,500 a kowace mita daya.
Bugu da kari, sakamakon irin muhimmancin da take da shi, hakan ya sa nau’ikanta ke ci gaba da bacewa ko kuma yin karanci a fadin duniya baki-daya.