Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu, ya yi alkawarin inganta tsaro, sauya tattalin arziki da sauransu, yayin da ya bayyana abubuwa uku da zai yi idan aka zabe shi a matsayin shugaban kasa a shekara mai zuwa.
Ya tabbatar wa shugaban kasa, Muhammadu Buhari kudirinsa na girmama kokarinsa da abubuwan da ya bari bayan wa’adinsa a 2023.
- PDP Ta Zargi Makiyan Dimokuradiyya Da Kitsa Hargitsi A Gangamin Da Jam’iyyar Ta Yi A Kaduna
- Rundunar Soji Sun Kashe Mayakan Boko Haram 6 A Borno
Tsohon gwamnan na Jihar Legas ya yi wadannan alkawuran ne a lokacin da ya gabatar da sakon fatan alheri a taron kwana uku na ministoci da sakatarorin dindindin da ke gudana a Abuja a ranar Talata.
Ya kuma yaba wa gwamnatin Buhari bisa yadda ta samar da mulki mai tsari ga kasar nan, inda ya bayyana cewa shugaban ya dora kasar nan a kan turba mai kyau bayan shekaru da dama da aka shafe ana fama da rashin adalci.
Tinubu ya ce zai yi sa’a, idan aka zabe shi, ya karbi ragamar mulki daga gwamnatin da ta taka rawar gani sosai, inda ya yi alkawarin dora wa daga inda gwamnatin Buhari ta tsaya.
“Ku tabbatar da cewa an rubuta tarihin zamanin Buhari daidai, domin ta hada tubalan ginin don dorewar makoma ta wadata, zaman lafiya, ci gaba iri-iri da tsaro.
“Saboda haka, ina farin ciki da aka ba ni sandar gadon shugaba Buhari a matsayin mai rike da madafun iko a jam’iyyarmu, kuma ina fatan a matsayina na dan takarar shugaban kasarmu.
“Shugaban kasa da membobin gwamnatinsa, bari in bayyana kamar haka: Idan aka zabe ni, zan ba da girmamawar da ta dace ga kokarinku da abin da kuka bari.
“Zan yi aiki cikin kyakkyawan hadin kai da manufar kasa wacce ta samar da kafa jam’iyyarmu tare da bayyana ayyukan gwamnatinku.
“Mafi muhimmanci, hanyoyin da gwamnatin Tinubu za su himmatu don kara kariya da wadata al’ummar Nijeriya saboda manufarmu ita ce samar da kyakkyawan tsarin gudanar da mulki da gyara ga kasarmu.
Da yake magana a kan taken, “Habaka Tsaro, Yaki da Cin Hanci da Rashawa, Sauya Tattalin Arziki’, Tinubu ya bayyana farin cikinsa da kasancewa daya daga cikin magoya bayan gwamnatin tun daga rana ta daya.
Ya yaba wa Buhari da majalisarsa kan rashin bai wa ‘yan Nijeriya kunya da suka yi imani da su.
“Na gode shugaba Buhari, a madadin daukacin ‘yan Nijeriya da daukacin gwamnatinka, da wanda duk ya halarci taron nan a yau ko ya wakilta, mun ba ka goyon baya tun daga ranar farko da ka hau mulki, zan ci gaba da kasancewa amininka kuma ko da bayan ka sauka.
“Na san irin hangen nesan da kuka yi wa Nijeriya. Na san irin sadaukarwar da kuka yi wa wannan al’umma. Na san abubuwan da kuka cimma.
“Zan iya fada muku cewar abubuwan da kuka yi suna da muhimmanci kuma masu dorewa ne,” in ji shi.