Assalamu alaikum masu karatu barkammu da sake haduwa da ku a wannan mako a cikin shirin namu mai farin jini da albarka na Ado da Kwalliya.
A yau shafin namu ya yo muku tsaraba ne da wani sirri da ke tattarai da Abarba wajen gyaran fata.
Za ku yi mamaki, babbar fa’idar Abarba da ake samu baya ga fa’idodin da take da su a bangaran inganta lafiyar jiki kamar shahararren sirrinta na narkar da abinci da kuma habaka rigakafi.
Abarba tana da matukar kyau da tasiri wajen inganta lafiyar jama’a gaba daya, amma baya ga haka abin da wannan kayan marmarin yake yi na musamman da yake da matukar mamaki shi ne abin da za mu zo da shi a rubutun namu na yau wanda yake da matukar kyau da amfani.
Wannan dan itace yana da isasshen sinadarin bitamin da sinadarin kara karfin kashi da sauran sinadarai irin su ‘Manganese’, ‘calcium’, ‘sodium’, da magnesium, wadannan duk suna cikin Abarba.
Binciken masana kiwon lafiya da masana bangaran magungunan da abinci ke yi ga dan’Adam sun tabbatar da cewa Abarba tana habaka lafiyar fata idan aka sha ta yadda take ko ta hanyar shafa ruwanta a-kai-a-kai. Ga sauran wasu sirrukan abin da Abarba ke yi ga dan’Adam:
Yaki da tsufa
Akwai mata da dama wadanda suke da shekaru a duniya amma sun tsani a rika yi musu kallon tsofaffi, to ina ire-iren wadannan matan, hanya mafi sauki da za ku rika yakar tsufanku ita ce ku rika shan Abarba a-kai-a-kai. Lallai bincike ya tabbatar da Abarba tana jinkirta saurin tsufa saboda sinadaran da take dauke da su na yaki da yamutsewar fata.
Tana rage duhu ko tabon baki a jiki
Abarba tana dauke da wadataccen sindarin ‘Ascorbric Acid’ wadda yake matukar taimakawa wajen yaki da tabon ciwo da ya yi baki a jiki. Haka nan idan kina son kawar da bakin da ba ki so a wata gaba ta jikinki, kawai ki shafa ruwan Abarba a kan wuraren da suke da duhun, ki barshi na tsawon mintuna biyar, sannan ki wanke da ruwan dumi, za ki sha mamaki cikin yardar Allah.
Barkewar kurajen fuska:
Har ila yau, wani sirri da Abarba take dauke da shi shi ne, kawar da kuraje masu sa duhu a fuska, ana ba da shawarar cewa idan mace tana son hana wadannan kurajen na fuska su bata mata kyan fuska ta rika shafa ruwan Abarba za ta samu za ta sha mamaki.
Gyara fata
Abarba tana kunshe da sinadaran ‘Enzymes’ wanda ke cire matattun kwayoyin halittar fata da kuma haskaka fata. Don haka, idan kina so fatarki ta kara haske (ba irin na bilicin ba), ki rungumi sha da shafa Abarba.
Tana taimaka wa warkar da raunuka.
Abarba tana da wani sinadari maganin ‘Antiodidant’, da na bitamin C wadanda suke iya taimakawa wajen hana lalacewar kwayoyin fata. Don haka idan aka yi amfani da ita tana iya taimakawa wajen saurin warkar da rauni ta hanyar tallafa wa samar da sabbin kwayoyin fata.
Ina fata mun amfana da wannan tsaraba. Sai kuma mako mai zuwa idan Allah ya kai mu.