Assalamu alaikum masu karatu barkammu da sake haduwa da ku a wannan makon a cikin shirin na mu mai farin jini da albarka na Ado da Kwalliya.
Ga mata masu fama da bakin fuska ko kuma gefai gefan fuska dayan biyu ne kina shafa cream kina shiga rana ko kina shafawa lokacin gari da zafi ko kina shafawa ki shiga aikin abinci ko kina shafa man da yayiwa fatarki karfi.
- Gwamnatin Gombe Za Ta Dauki Sababbin Ma’aikatan Lafiya 200
- Manchester City Ta Fara Kakar Wasa Ta Bana Da Kafar Dama
Yadda za ki magance wannan tabon za ki samu madara ta ruwa sai ki sata a furiji ta yi sanyi so sai sai ki goga a wannan tabo naki ya yi kamar minti ashiri ko fi haka sai ki wanke sannan idan gari da zafi za ki samu ruwan sanyi ki samu ‘yar audiga na bolls ki tsoma a ruwan sanyi sai dora a kan tabon za ki barshi ya yi kamar minti biyar haka sai ki cire audugar ki shafa mai idan kika yi wannan kamar sau uku haka sai kina yi fuskarki gaba daya inshaAllahu za ki ga canjin fuskarki ta dawo dai dai inshaAllah za ki yi mamaki.
Sannan za ki iya nema dutu bilicin forodut ko sanbo shima idan kina amfani da su yana gyara fuska so sai.