Bisa ƙoƙarinta na son samar da kuɗaɗen shiga da yawansu ya kai kimanin Naira tiriliyan 3.9 a duk shekara, gwanatin tarayya ta ƙaddamar da tsari da kuma haɗakar norman waken soya.
Gwamanatin, ta yi hakan ne bisa manufar samar wa da fannin alƙibla mai ɗorewa da kuma ƙara ɗora ƙasar kan turbar aikin noma a fannin duniya.
Tsarin ya ƙunshi abubuwa bakwai da suka haɗa da samar da ingantaccen Irin Waken Soya, ƙasar noma ta kimiyya da ayyukan malaman gona.
- An Nuna Fasahar Waken Pingtan Na Kasar Sin A Najeriya
- Dalilin Da Ya Sa Farashin Wake Ba Zai Sauka Ba A Nijeriya -Masana
Sauran su ne, samar da kayan aikin noma na zamani, samar da kayan aikin noma masu yaƙar sauyin yanayi, faɗaɗa gonakan yin noma da kuma sama wa masu nomansa kasuwa.
Wannan bayani ya fito ne daga bakin Babban Ministan Aikin Gona da Samar da Wadataccen Abinci, Sanata Abubakar Kyari, a wajen taron ƙaddamar da tsarin da aka gudanar a Abuja.
Kyari ya ce, a yanzu ana noma Waken Soya da ya kai kimanin tan miliyan 1.35, wanda kuma buƙatar da ake da shi a ƙasar ya wuce tan miliyan 2.7.
Ya sanar da cewa, wanan tsari zai kuma amfani tattalin arziƙin ƙasar da ƙara samar da ayyuakn yi da kuma ƙara haɓaka samar da wadataccen abinci a ƙasar.
Shi kuwa a nasa jawabin a wajen ƙaddamarwar, Gwamnan Jihar Biniwai, Hyacinth Iormem Alia, ya jaddada muhimmancin da za a amfana da shi a tsarin.
“Dabarun faɗaɗa noman Waken Soya na ƙasa, mataki ne da ya dace wajen yin haɗaka, domin samar da kuɗaɗen shiga ga ƙasar a duk shekara da suka kai kimanin Naira tiriliyan 3.9 da ƙara ƙirƙiro da ayyukan yi a ɗaukacin jihohi 22, ciki har da Abuja, wanda hakan zai kuma ƙara ɗaga martabar Nijeriya a idon duniya a fannin aikin noma”, in ji Hyacinth.
Ya kuma goyi bayan shirin ruɓanya samar da ingantaccen Irin Waken Soya da kuma rabar da shi ga sama da masu nomansa kimanin 200,000, nan da shekara uku masu zuwa.
“Wannan tamkar kira ne na fara gudanar da wani, kuma kira ne ga al’ummominmu da ke karkara da kuma ƙanannan manoma har ga tattalin arziƙin ƙasarmu” a cewar gwamnan.
Ya sanar da cewa, tun lokacin da aka gabatar da samfurin Waken Soya na ‘Malayan’ a shekarar 1937, albarkar ƙasar noma ta Guinea Saɓanna, hakan ya sanya manoma a yankin, ƙara mayar da hankali wajen nomansa, saboda irin dausayin da ƙasar noman ke da shi.
“Ƙasar noma ta Jihar Biniwai, cike take da albarka, wanda hakan ya bai wa jihar damar kasancewa kan gaba wajen noman Waken Soya a Nijeriya da ma Afirka ta Yamma baki-ɗaya,” in ji gwamnan.
Har ila yau, gwamnan ya bayyana cewa; jiharsa na da ƙudurin ruɓanya noman na Waken Soya daga tan 202,000 zuwa aƙalla tan 400,000, nan da shekara uku masu zuwa, wanda hakan zai ba ta damar noma Waken sama da tan 400,000 a duk shekara.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp