• English
  • Business News
Wednesday, September 17, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Abubuwan Da Ya Kamata A Sani A Gasar Cin Kofin Afirka

by Abba Ibrahim Wada
2 years ago
in Wasanni
0
Abubuwan Da Ya Kamata A Sani A Gasar Cin Kofin Afirka
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Labarai Masu Nasaba

Barcelona Ta Farfaɗo Zuwa Matsayi Na Biyu Bayan Lallasa Valencia A Johan Cruyff

Kano Pillars Ta Samu Nasarar Farko A Gasar Firimiyar Nijeriya Ta Bana

Kamar dai yadda hukumar kwallon kafa ta Nahiyar Turai ta bayyana, za a fara gasar ta cin kofin Afirka karo na 34 daga ranar 13 ga Janairu zuwa 11 ga watan Fabrairun 2024.

Karo na biyu ke nan da Ibory Coast za ta karbi bakuncin wasannin bayan na farko da ta karba a shekarar 1984 sai dai da farko, an tsara yin gasar daga watan Yuni zuwa Yulin shekara 2023 amma daga baya aka sauya wasannin saboda fargabar da ake da ita kan buga gasar a tsakiyar damuna.

  • Sin Za Ta Fadada Girman Tashar Binciken Samaniyarta
  • Gwamna Uba Sani Ya Taya Sarkin Zazzau Murnar Cika Shekara Uku A Kan Karagar Mulki 

Gasar za ta ci gaba da amsa takenta na 2023 duk kuwa da cewa za a buga ta ne a shekarar 2024 kuma wasan farko zai kunshi tawagar mai masaukin baki, wadda za ta fito cikin rukunin farko da za a hada ta da wasu tawagogin kasashe.

Kungiyoyin da suka yi na daya da na biyu a kowanne rukuni za su kai zagayen ‘yan 16, da wasu wadanda suka hada maki da yawa, amma suka kare a mataki na uku a rukuni daga shida da za a raba dauke da kasashe hudu kowanne – daga nan a buga wasan kusa da na kusa da na karshe da na dab da na karshe da karawar neman mataki na uku da kuma fafatawar karshe.

Filin wasa na Alassane Ouattara da ke Birnin Abidjan ne zai karbi bakuncin karawar karshe a ranar 11 ga watan Fabrairu, kamar yadda hukumar kwallon kafar Afirka CAF ta tabbatar.

Kusan wata daya za a kwashe ana fafatawa daga watan Janairu zuwa Fabrairu, inda fitattun ‘yan kwallo za su yi fatan lashe kofin babbar gasar kofin Afirka da hukumar CAF kan shirya.

Mai rike da kofin AFCON, Senegal za ta kira fitattun ‘yan kwallonta kamar Sadio Mane da ke wasa a Al-Nassr da na Chelsea, Nicolas Jackson, yayin da Masar, wadda ke kan gaba a yawan daukar kofin har karo bakwai – za ta kasance da kyaftin dinta mai buga wasa a Liberpool, Mohamed Salah.

Gasar ta wannan shekarar za ta kunshi kasashe 24, kuma a karo na uku, bayan an kara fadada wasanninta a 2019 kuma duk da yake Ibory Coast ce mai masaukin baki, amma ta buga wasannin neman shiga gasar, inda ta yi ta biyu a rukuni na takwas da Zambia ta ja ragama.

Kasashen biyu sun hade da 22 da suka yi na daya da na biyu a kowanne rukuni inda jimilla suka zama kasashe 24 domin fafatawa a wasannin da za a buga, sannan dukkan kasashen da za su je Ibory Coast sun fafata a gasar kofin Afirka biyu a baya, in ban da Zambia, wadda ta lashe gasar a 2012, kuma za ta buga gasar a karon farko bayan 2015 da kuma wadda za ta kara karo na biyar, rabonta da gasar dai tun a 2010.

Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya ta kusan shiga gasar a karon farko, amma ta barar da damar bayan ta yi rashin nasara a hannun Ghana, wadda ke sama da ita sai dai kasar Gabon ita ce fitacciyar kasa da ba za ta je gasar ba.

Za a raba jadawalin gasar ne a birnin Abidjan ranar 12 ga watan nan na Oktoba da karfe 7 na yamma agogon GMT, kuma za a yi la’akari da kwazon tawagogin a jerin gwanayen kasashen kwallon kafa da FIFA kan fitar, kuma kasashe 24 aka raba zuwa tukunya hudu.

Amma kuma Kasar Ibory Coast yanzu haka tana mataki na tara a kan gaba a kwallon kafa a Afirka, ita ma an saka ta a tukunyar raba rukuni saboda ita ce mai masaukin baki.

Yadda Za’a RabaJadawalin:

Tukunyar farko – Ibory Coast (50), Morocco (13), Senegal (20), Tunisia (29), Algeria (34), Egypt (35)

Tukunya ta biyu – Nigeria (40), Cameroon (41), Mali (49), Burkina Faso (58), Ghana (60), DR Congo (64)

Tukunya ta uku – South Africa (65), Cape Berde (71), Guinea (81), Zambia (82), Ekuatorial Guinea (92), Mauritania (99)

Tukunya ta hudu – Guinea-Bissau (106), Mozambikue (113), Namibia (114), Angola (117), The Gambia (118), Tanzania (122)

Za a raba kasashen zuwa rukuni shida da za su kunshi kasashe hurhudu kowanne, sannan kuma za a sanar da raneku da lokutan da za a fafata wasanni a Gasar ta AFCON 2023.

Filayen da za a buga wasannin:

Alassane Ouattara Stadium, Abidjan (Mai cin ‘yan kallo 60,000), Felid Houphouet Boigny Stadium, Abidjan (Mai cin ‘yan kallo 33,000) Stade de la Paid, Bouake (Mai cin ‘yan kallo 40,000) Amadou Gon Coulibaly Stadium, Korhogo (Mai cin ‘yan kallo 20,000)

Laurent Pokou Stadium, San Pedro (Mai cin ‘yan kallo 20,000) Charles Konan Banny Stadium, Yamoussoukro (Mai cin ‘yan kallo 20,000)

Hukumar kwallon kafa ta Afirka CAF na gayyatar fitattun ‘yan kwallon Nahiyar a lokacin da take gabatar da jadawalin kuma a wannan shekarar ma ana sa ran za a ga fitattun ‘yan wasan Ibory Coast, kamar Kolo Taure da dan uwansa Yaya Toure, wadanda suka buga wa kasar wasa, kuma suka doke Ghana kafin gasar a Kofi na biyu da Ibory Coast ta dauka a 2015.


Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

ShareTweetSendShare
Previous Post

‘Yan Afirka Ta Kudu Sun Bayyana Dalilansu Na Kyamar Baki

Next Post

Dagwalon Nukiliyar Japan: Kar Duniya Ta Rungume Hannu Kilu Ta Ja Bau

Related

Barcelona Ta Farfaɗo Zuwa Matsayi Na Biyu Bayan Lallasa Valencia A Johan Cruyff
Wasanni

Barcelona Ta Farfaɗo Zuwa Matsayi Na Biyu Bayan Lallasa Valencia A Johan Cruyff

2 days ago
Kano Pillars Ta Samu Nasarar Farko A Gasar Firimiyar Nijeriya Ta Bana
Wasanni

Kano Pillars Ta Samu Nasarar Farko A Gasar Firimiyar Nijeriya Ta Bana

3 days ago
Sama Da Fam Biliyan Uku Aka Kashe A Firimiyar Ingila Wajen Sayen Ƴan Wasa
Wasanni

Sama Da Fam Biliyan Uku Aka Kashe A Firimiyar Ingila Wajen Sayen Ƴan Wasa

3 days ago
Me Ya Sa Bayern Liverkusen Ta Kori Erik Ten Hag Bayan Wasanni Biyu?
Wasanni

Me Ya Sa Bayern Liverkusen Ta Kori Erik Ten Hag Bayan Wasanni Biyu?

3 days ago
Ba Lallai Ne FIFA Ta Cirewa Afrika Ta Kudu Maki 3 Ba – Rayond Hack
Wasanni

Ba Lallai Ne FIFA Ta Cirewa Afrika Ta Kudu Maki 3 Ba – Rayond Hack

5 days ago
Nijeriya Ta Rasa Tikitin Kai Tsaye Na Zuwa Gasar Kofin Duniya 
Wasanni

Nijeriya Ta Rasa Tikitin Kai Tsaye Na Zuwa Gasar Kofin Duniya 

1 week ago
Next Post
Dagwalon Nukiliyar Japan: Kar Duniya Ta Rungume Hannu Kilu Ta Ja Bau

Dagwalon Nukiliyar Japan: Kar Duniya Ta Rungume Hannu Kilu Ta Ja Bau

LABARAI MASU NASABA

Yanzu-yanzu: Shugaba Tinubu Ya Ɗage Dokar Ta-ɓaci A Jihar Ribas

Yanzu-yanzu: Shugaba Tinubu Ya Ɗage Dokar Ta-ɓaci A Jihar Ribas

September 17, 2025
Guterres: Jerin Shawarwarin Da Sin Ta Gabatar Sun Cika Ka’idar Kundin Tsarin Majalisar Dinkin Duniya

Guterres: Jerin Shawarwarin Da Sin Ta Gabatar Sun Cika Ka’idar Kundin Tsarin Majalisar Dinkin Duniya

September 17, 2025
NECO Ta Saki Sakamakon Jarrabawar 2025

NECO Ta Saki Sakamakon Jarrabawar 2025

September 17, 2025
Lakurawa Sun Hallaka Jami’in Kwastam A Jihar Kebbi

Lakurawa Sun Hallaka Jami’in Kwastam A Jihar Kebbi

September 17, 2025
Sojoji Sun Kashe Mayaƙan ISWAP 11 A Borno Da Adamawa

Sojoji Sun Kashe Mayaƙan ISWAP 11 A Borno Da Adamawa

September 17, 2025
‘Yan Bindiga Sun Sace Mutum 7 A Jihar Neja

‘Yansanda Sun Kama ‘Yan Ƙungiyar Asiri Da Ɓarayin Kifi A Jihar Neja

September 17, 2025
Mataimakin Shugaban Jam’iyyar APC Na Nasarawa, Aliyu Barde, Ya Rasu

Mataimakin Shugaban Jam’iyyar APC Na Nasarawa, Aliyu Barde, Ya Rasu

September 17, 2025
Sowore Ya Maka DSS, Meta da X A Kotu Kan Take Masa Haƙƙi

Sowore Ya Maka DSS, Meta da X A Kotu Kan Take Masa Haƙƙi

September 17, 2025
Saudiyya Ta Saki ‘Yan Nijeriya 3 Da Aka Yi Wa Sharrin Safarar Ƙwayoyi

Saudiyya Ta Saki ‘Yan Nijeriya 3 Da Aka Yi Wa Sharrin Safarar Ƙwayoyi

September 17, 2025
Babban Jirgin Ruwan Kasar Sin Ya Nufi Yankin Tekun Kudancin Kasar Domin Gwaji Da Samar Da Horo

Babban Jirgin Ruwan Kasar Sin Ya Nufi Yankin Tekun Kudancin Kasar Domin Gwaji Da Samar Da Horo

September 16, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.