Kungiyar Dattawan Arewa (ACF), ta ce kada a dauki kungiyar ta’addancin ta Lakurawa da wasa ko kuma a bar ta cikin al’umma kamar yadda aka yi sakaci da batun Boko Haram da rikicin manoma da makiyaya da masu garkuwa da mutane.
A ranar Juma’ar da ta gabata sai da mayakan Lakurawa suka kashe mutum 15 a kusa da garin Mera a Karamar Hukumar Augie da ke Jihar Kebbi.
- Ta Hanyar CIIE Duniya Ta Kara Fahimtar Matakan Sin Na Samar Da Abubuwa Da Aka Fi Tsananin Bukata
- Masanan Afirka Na Dakon Halartar Shugaba Xi Taron Koli Na G20
Ƙungiyar Dattawan Arewa ta bukaci sojojin Nijeriya su yi kokari wajen murkushe sabuwar kungiyar ta’addancin wato Lakurawa wadda ta bulla a jihohin Sakkwato da Kebbi.
ACF ta bayyana haka ne cikin wata sanarwa da ta fitar mai dauke da sa hannun sakataren watsa labaranta, Farfesa Tukur Muhammad Baba.
Ta bukaci sojoji su yi amfani da duk wasu kayan aiki domin tabbatar da cewa sun murkushe ‘yan ta’addan.
Kungiyar ta ce bullar wannan sabuwar kungiyar ta Lakurawa ta jawo bukatar kafa wata sabuwar rundunar kawance ta kasa da kasa tsakanin Nijeriya da makwabta.
A cewarya akwai bukatar a samu hadin kan Jamhuriyar Nijar wajen sanya kanta a ciki.
“Akwai bukatar a yi amfani da ziyarar da babban hafsan tsaro na Nijeriya, Janar Christopher Musa ya kai Jamhuriyar Nijar a farkon wannan shekarar a matsayin wata dama don kokarin da ake yi na kasa da kasa domin murkushe ta’addanci,” in ji sanarwar.
Yanzu haka hukumomi a Nijeriya sun ayyana kungiyar Lakurawa a matsayin ‘yan ta’adda.