Ƙungiyar Kiristocin Nijeriya (CAN) ta fitar da sabon adadi na ɗalibai da malamai da aka sace daga makarantar St. Mary da ke Papiri, ƙaramar hukumar Agwara, jihar Neja, inda ta tabbatar cewa adadin ya kai 315. A cikin wata sanarwa da ta fitar, ƙungiyar ta ce adadin farko na 227 da aka ambata jiya ba daidai ba ne, bayan gudanar da cikakken bincike.
CAN ta bayyana cewa daga cikin waɗanda aka sace akwai ɗalibai 303 da malamai 12. Ta ce a lokacin da aka watse daga makarantar domin gujewa faɗawa hannun mugayen, wasu sun yi ƙoƙarin tserewa, inda daga baya suka gano an kama ƙarin mutane 88 da ke ƙoƙarin tserewa.
- Matsalar Tsaro: Majalisar Wakilai Ta Nemi Tinubu Ya Canza Salon Yaki
- Japan Ba Ta Cancanci Neman Kujerar Dindindin A Kwamitin Tsaron MDD Ba
“Jimillar mutanen da aka sace daga makarantar St. Mary, Papiri, shi ne ɗalibai 303 da malamai 12,” in ji CAN. Ƙungiyar ta ce wannan ƙarin adadi ya bayyana ne ne bayan ƙarin bincike da aka gudanar, da kuma roƙon da ta yi ga iyaye da hukumomin tsaro su tura cikakken bayanai kan lamarin.
CAN ta buƙaci ƙarfafa ƙoƙarin ceto waɗanda aka sace da saurin kawo ƙarshen irin waɗannan hare-hare. Ta kuma yi kira ga gwamnati da jami’an tsaro su samar da tsaro ga makarantu, musamman na addinai, domin kare rayukan yara da malamai daga farmakin ƙungiyoyin ƴan ta’adda.













