Yau Alhamis, ma’aikatar kasuwanci ta kasar Sin, da hukumar kididdiga ta kasar Sin, da hukumar kula da musayar kudade ta kasar Sin, sun gabatar da rahoton “jarin da kasar Sin ta zuba kai tsaya a kasashen ketare a shekarar 2022”. Rahoton ya bayyana cewa, a shekarar 2022, adadin jarin da kasar Sin ta zuba kai tsaye a ketare ya kai dalar Amurka biliyan 163 da miliyan 120, adadin da ya kasance matsayi na biyu a duk fadin duniya, kuma ya kai matsayin dake kan gaba a wannan fanni cikin shekaru 11 a jere, adadin da ya zarce kashi 1 bisa 10 na jarin da kasashe suka zuba a ketare cikin shekaru 7 a jere.
Kuma, a karshen shekarar 2022, masu zuba jari na kasar Sin sun kafa kamfanoni dubu 47 a kasashe da yankuna 190, kuma kaso 7.1 bisa dari daga cikinsu suna kasashen Afirka, yayin da aka kafa kamfanoni guda dubu 16 a cikin kasashen da suka hada kai da kasar Sin wajen aiwatar da shawarar “Ziri daya da hanya daya”.
Har ila yau a shekarar 2022, yawan harajin da kamfanonin kasar Sin dake kasashen waje suka biya kasashen ya kai dalar Amurka biliyan 75, adadin da ya karu da kaso 35.1 bisa dari. Kuma, ya zuwa karshen shekarar 2022, adadin ma’aikatan dake aiki a kamfanonin kasar Sin a kasashen ketare ya wuce miliyan 4 da dubu 100, ciki hada da ma’aikata ‘yan asalin kasashen kimanin miliyan 2 da dubu 500. (Mai Fassara: Maryam Yang)