Kafar CMG ta rawaito alkaluman babban gidan wayar kasar Sin dake nuna yadda sashen aikewa da kunshin sakwanni na kasar, ya yi hada hadar aikewa da kunshi biliyan 15.8 a watan Yulin da ya gabata, adadin da ya karu da kaso 20.1 bisa dari idan aka kwatanta da na Yulin bara.
Cikin adadin, kayayyakin da aka jigilar cikin sauri sun kai kunshi biliyan 14.26, adadin da ya karu da kaso 22.2 bisa dari kan Yulin bara.
Bugu da kari, daga watan Janairu zuwa Yulin bana, hada hadar da sashen aikewa da sakwannin ya gudanar ta kai kunshi biliyan 105.23, karuwar kaso 20.4 bisa dari a shekara. Ciki har da kayayyakin da aka jigila cikin gaggawa da yawan su ya kai kunshi 94.42 bisa dari, karuwar da ta kai ta kaso 23.0 bisa dari a shekara. (Mai fassara: Saminu Alhassan)