Aƙalla mutane 52 ne suka rasa rayukansu a wani sabon hari da ’yan bindiga suka kai wasu ƙauyuka a ƙaramar hukumar Bokkos da ke Jihar Filato.
’Yan bindigar sun kai hari a ranar 2 ga watan Afrilu, 2025, inda suka farmaki ƙauyukan Mangor Tamiso, Daffo, Manguna, Hurti da Tadai.
- APC Ta Musanta Zargin Sauya Kashim Shettima A Zaɓen 2027
- Ana Zargin Wani Ɗansanda Da Kisan Wata Mata Kan Cin Hancin Naira 2,000 — Bincike
Har yanzu ana ci gaba da gano gawarwakin waɗanda suka rasu a dazuka da ke kewaye da yankin.
“Muna birne mutane 31 ranar Alhamis. Yara biyar sun ƙone kurmus a Hurti, an kashe mutane 11 a Ruwi, hudu a Manguna, sai daya a Dafo,” in ji Farmasum Fuddang, shugaban ƙungiyar ci gaban al’ummar Bokkos.
Gwamnatin jihar ta tabbatar da kama wasu da ake zargi da hannu a harin, tare da ƙara tsaro a yankunan da abin ya shafa.
“Muna yin duk mai yiwuwa don ganin an kama waɗanda suka aikata wannan ɗanyen aiki,” in ji Kwamishinar Yaɗa Labaran, Hon. Joyce Ramnap.
“Muna roƙon jama’a da su kwantar da hankalinsu, su riƙa kai rahoton duk wani abun zargi, su kuma guji ɗaukar doka a hannunsu.”
Gwamnatin ta kuma buƙaci shugabannin addinai da na gargajiya da su ci gaba da wayar da kan jama’a kan muhimmancin zaman lafiya da haɗin kai.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp