A gobe Juma’a, 23 ga watan Nuwamba, 2023, kungiyar gwamnonin jihohin Arewa maso gabashin Nijeriya, za ta gudanar da taronta karo na 9 a jihar Adamawa.
Gamayyar Jihohin da suka hada kungiyar, sun hada da Borno, Bauchi, Adamawa, Gombe, Yobe da Taraba. Kungiyar tana taronta ne duk bayan watanni shida.
- NNPP Ta Bukaci Majalisar Shari’a Ta Kasa Ta Binciki Hukuncin Da Aka Yanke Wa Gwamna Yusuf
- Dan Majalisa Zai Aurar Da Mata Marayu 100 A Kebbi
A duk lokutan gudanar da taron kungiyar, gwamnonin sun fi mayar da hankali ga matsalolin da yankin ke fuskanta a dunkule, kama daga matsalar fatara da koma-baya, karancin ababen more-rayuwa, tsaro da tattalin arziki.
To sai dai, har kawo lokacin hada wannan rahoton, babu cikakken bayani akan abinda taron na 9, kuma na farko tun bayan gudanar da zaben 2023, zai fi mayar da hankali.