Hakika lamarin jagorancin jama’a a lokacin mulkin dimokuradiyya yana tafiya ne da adawa. Sai dai kuma idan za a yi adawar, ya dace a yi mai ma’ana wadda hankali ke dauka, domin adawa a tafarkin ilimi ita ce gishirin siyasa.
Lallai an yi adawa a lokacin gwamnatin, Alhaji Attahiru Dalhatu Bafarawa ta APP/ANPP (1999-2003), inda a lokacin, su Hon. Abubakar Shehu Tambuwal da Hon. Arzika Tureta (marigayi) suke a sahun gaba wajen yin adawa a karkashin tutar jam’iyyar PDP (wadda ke rike da gwamnatin tsakiya). Sai dai a lokacin babu kafafen sadarwa na soshiyal midiya irin yanzu. Hasali ma kila ko da akwai su, ba za a yi adawa ta wuce-wuri da cin mutuncin juna irin ta yanzu.
- Ƙaramin Ministan Tsaro Da Manyan Shugabannin Soji Sun Isa Sokoto Domin Fatattakar ‘Yan Bindiga
- Ambaliyar Ruwa Ta Lalata Gidaje 14,940 A Sokoto
Abin da aka al’adanta ne cewa wanda ake yi ma adawa idan ya tsima a fagen siyasa, wani sa’ilin ya kan iya janye abokan adawarsa su dawo bangarensa. Hakan ya faru a lokacin gwamnatin Bafarawa, inda ya yi nasarar janye Alhaji Abubakar Shehu Tambuwal ya dawo jam’iyyarsa. Hakan ma ta faru a lokacin Gwamna Aliyu Magatakarda Wamakko, inda ya janye Usman Sulaiman (Dan-Madamin Isa) daga wancan bangaren na Bafarawa zuwa nasa. Ko a haka da ake yanzu, wa ya san gobe ban da Allah (SWA)? Hausawa kan ce Sarki goma zamani goma.
Abin da wani shugaba kan iya jurewa na adawa, wani ba zai dauka ba. Kuma inda wani ya yi rawa aka yi mai kari, wani idan ya yi, kashi zai sha. A bayyane take cewa a nan jiharmu ta Sakkwato, ana wuce gona da iri wajen amfani da soshiyal midiya wajen yin adawa wadda take da sigar cin zarafi da shiga rigar mutuncin juna har da na iyali. Kuma fa an lura da cewa kowane bangare ya sami dama, yi yake, amma ga abin da ya bayyana a halin yanzu, dayan bangaren na masu adawa ya fi zakewa.
An tabbatar da cewa a tarihin siyasar Sakkwato, ba a yi gwamna mai juriyar sukar adawa ba kamar Barista Aminu Waziri Tambuwal, wanda ya sauka jiya-jiya. Me ya sa a Sakkwato ba a koyi da salon adawar siyasa ta makwabtan jihohinmu na yankin kudu? A tasu salon adawar siyasa, iya sarrafa harshen Turanci da tajwidinsa ko akasin haka ba su ne abin suka ba ga shugaba, sai dai salon jagoranci da wanzar da ayyukka da ke da tasiri ga jama’a, ko bin diddigin ajandar da dan takara ya bayyana a lokacin neman kuri’un jama’a, da sauransu.
A wani bangaren kuma, za a iya cewa, sai bango ya tsage, kadangare ke samun kafar shiga. Gwamnatinmu ta Sakkwato na bukatar kimtsa gidanta musamman a tawagar kafar sadarwa (media team), sabanin gwamnatocin da suka gabata na Bafarawa da Wamakko da Tambuwal inda kowace daga cikinsu na da gwargwadon kwararrun masana masu aiki kafada da kafada a tawagar masu rubuta jawabi (speech writing team) da ababen da suka shafi fitar da bayanai (Press release) da aka tantance sosai don kauce wa tuntuben alkalami da sako mai harshen damo da sauransu.
Idan ko akwai ayarin kwararrun masanan, to kila ba a ba su cikakkiyar damar yin aiki tare ba don abin ya yi armashi domin kuwa hannu daya ba ya daukar jinka.
Idan kuma aka zo bangaren ganawa da uban tafiyar, watau gwamna, nan ma akwai bukatar gyara sosai. A inda aka fito, lokacin da gwamnatin nan na kan turbar adawa, ganawa da Tambuwal na daya daga cikin kalubalolin da ake sukarsa da su domin ko kwamishinoninsa ba su faye samun ganawa da shi ba a lokacin da suke so. Bincike ya tabbatar da cewa duk kanwar ja ce, domin babu bambancin jiya da yau, inda hasali ma, ko hadiman Gwamna Dakta Ahmad Aliyu mai ci yanzu, shakku suke wajen yi wa mutum iso ko neman damar ganawa da shi.
Sai kuwa idan shi gwamnan ne ke da bukata da ganinka. Haka abin yake ga mukarraban gwamnatin, domin kuwa kalilan daga ‘yan majalisar jihar ke da juriyar sauraren jama’arsu a ofis ko a gida kamar yadda ya dace. Wannan ya saba wa a kalla gwamnoni biyu da aka yi kafin Tambuwal da Ahmad. Domin kuwa ana iya ganawa da Bafarawa a ofis ko gida a wancan lokacin da yake gwamnan Jihar Sakkwato. Shi Aliyu Wamakko sha-kundum ne domin kusan kowa na iya ganawa da shi a ko ina ta kama sa’ilin da yake gwamna. Ashe kuwa kyawon da ya gaji ubansa.
Ai ba kowa ne zai ce sai ya gana da gwamna ba, sai wanda ke ganin matsayinsa ya kai. Wannan sanken ne ke kawo shakku ga manyan ‘yan bokonmu da sauran masana a Sakkwato da ke da zimmar zuwa don bayar da shawara ga gwamnan ko ‘yan majalisarsa. Akwai ma bayanan da ke nuna cewa galibin kwamishinonin gwamnatin Sakkwato ba su daukar waya ko da ta wanda suka sani ce. Da fatar za a gyara.
Daga Dakta Sajo Sanyinna, malami ne a jami’ar Usmanu Danfodiyo kuma tsohon shugaban kungiyar ‘yan jarida ta kasa reshen Jihar Sakkwato