Jam’iyyar hamayya ta ADC, ta zargi wasu jami’an gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ƙulla makirci don tarwatsa haɗin kansu kafin zaɓen 2027.
A cikin wata sanarwa da kakakin jam’iyyar na riƙon ƙwarya, Mallam Bolaji Abdullahi, ya fitar a ranar Litinin, ADC ta ce tana da bayanan sirri cewa an shirya wata ganawa a ɓoye da tsofaffin shugabannin jam’iyyar daga yankunan Arewa Maso Gabas da Arewa Maso Yamma da kuma wasu manyan jami’an Gwamnatin Tarayya.
- Asibiti Mai Zaman Kansa A Kano Zai Fara Aikin Manyan Tiyatu Tare Da Rage Kuɗi Kaso 50%
- Zan Yaƙi Duk Wanda Ya Yi Sata Idan Na Zama Shugaban Ƙasa — Atiku
Jam’iyyar ta ce manufar wannan ganawa ita ce a ɓata lamarin sabbin shugabannin ADC da kuma haddasa rikici a cikin jam’iyyar domin hana ta ci gaba da zama ƙwararriyar jam’iyyar hamayya.
A cewar ADC: “Wannan ba siyasa ba ce, wannan makirci ne na hana ci gaban dimokuraɗiyya.”
Jam’iyyar ta buƙaci Shugaba Tinubu da ya ɗauki mataki kan waɗanda ke gudanar da wannan shiri, yana mai cewa idan ba a dakatar da su ba, hakan zai nuna cewa gwamnatin ba ta da kishin dimokuraɗiyya.
ADC ta tunatar da Tinubu cewa da gwamnatin Goodluck Jonathan ba ta jure hamayya ba a baya ba, shi ma ba zai kai matsayin shugaban ƙasa ba, kuma APC ba za ta lashe zaɓe ba.
Jam’iyyar ta ce ya kamata shugaban ƙasa ya nuna cewa yana goyon bayan gaskiya da ‘yancin jam’iyyu a tsarin dimokuraɗiyya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp