Gwamnan Jihar Ribas, Siminalayi Fubara, ya karrama golan Nijeriya, Stanley Nwabali, kan irin bajinta da kwazon da ya nuna a gasar kofin ƙasashe Afirka ta AFCON da aka kammala makon da ya gabata.
BBC ta rawaito cewa, An gudanar da bikin karrmawar a gidan gwamnatin jihar, gwamna Fubara ya bai wa golan – wanda ɗan asalin jihar – kyautar zunzurutun kuɗi naira miliyan 20.
- AFCON 2023: Tinubu Zai Karɓi Baƙuncin Tawagar Super Eagles A Fadarsa Da Ke Abuja Yau Talata
- AFCON 2023: Muna Alfahari Da Yadda ‘Yan Wasan Super Eagles Suka Wakilci Nijeriya – Tinubu
Haka kuma gwamnan ya karrama shi da lambar yabo ta DSSRS, lambar yabo ta biyu mafi daraja da ake bai wa wadanda suka yi bajinta a fannoninsu, da manyan ‘yan siyasa a jihar.
Gwamnan ya kuma bai wa tawagar Super Eagles da ta samu wakilcin kocin tawagar Jose Peseiro da Finidi George kyautar naira miliyan 30, sakamakon bajintar da ƙungiyar na nuna a gasar.
Nijeriya dai ta ƙare gasar a matsayi na biyu, bayan da ta sha kashi a hannun Ivory Coast mai masaukin baƙi da ci 2-1 a wasan ƙarshe.