Barkan mu da sake saduwa da ku Uwargida
A yau na kawo muku yadda ake hada masar dankalin Turawa domin yin abin buda-baki idan an kai Azumi. Tare da fatan za a gwada irin wadannan girke-girken da muke kawo muku.
Abubuwan da ake bukata
Dankalin Turawa, Attarugu, Albasa, Kwai, Gishiri da Magi, sai Kuma Kori
Ga kuma yadda ake hadawa
Bayan uwargida ta fere dankalinta, sai ta dora shi a wuta ya nuna ya yi luguf sosai, sannan sai ta dauko roba ko kwano mai zurfi ta zuba a ciki, sannan ta debo kwai mai dan dama ta fasa a kan dankalin sai ta samu ludayinta ta dama dankalin da kwan har sai sun hadu sosai.
Sai a debo albasa da attarugu a jajjaga su sannan a zuba a kan hadin dankalin da magi da gishiri da kori dai-dai kayan dandano, sannan sai a sake dama hadin domin kayan hadin su shiga dankalin sosai.
Idan uwargida ta gama hakan, sai ta dauko Tanda ta dora a kan wuta. A zuba man gyada a kowane gida, sannan a debo kullin dankalin a zuba a kowane gidan Tandar. Sai a dan ba shi mintuna domin dahuwar cikin masar. Idan gefe daya ya yi, sai a sake juya wainar zuwa dayan gefen har sai ta nuna kafin a sauke daga wuta.
A ci dadi lafiya.