Shugaban Nijeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya yabawa ‘yan wasan tawagar kwallon kafar Nijeriya bayan sun kai wasan karshe a kofin gasar Afirika da ake ci gaba da gudanarwa a kasar Cote de’Voire.
Shugaba Tinubu ya bayyana haka a wani rubutu da ya yi a shafinsa na Facebook a yau Laraba bayan kammala wasan da Super Eagles tayi nasara akan Bafana Bafana na kasar Afirika ta Kudu.
Yanzu Nijeriya tana jiran wanda zai yi nasara a tsakanin kasashen Congo da Ivory Coast a daya wasann kusa da na karshe, inda take neman lashe kofin a karo na hudu.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp