Tawagar Super Eagles ta Nijeriya ta tsallaka zuwa matakin dabda kusa da zagayen karshe a gasar cin kofin Afirika da ake ci gaba da bugawa a kasar Cote de’Voire.
Hakan ya faru ne bayan doke kasar Kamaru da ci 2-0 Haphoute Boigny da ke Abidjan.
- AFCON 2023: Super Eagles Ta Tsallake Zuwa Zagaye Na 16 Bayan Doke Guinea-Bissau
- AFCON 2023: Tauraron Super Eagles Na Fama Da Guba Gabanin Wasa Da Cote d’Ivoire
Dan wasan Nijeriya da ke buga wasa a kungiyar kwallon kafa ta Atalanta ta kasar Italiya, Ademola Lookman, ne ya jefa kwallaye biyu a ragar Kamaru.
Hakan yasa Nijeriya ta zama kasa ta biyu da ta tsallaka zuwa matakin dabda da kusa da zagayen karshe a gasar AFCON ta bana, bayan kasar Angola da ta doke Nambiya da ci 3-0.