Mataimakin shugaban ƙasar Nijeriya, Kashim Shettima, ya bar Abuja zuwa ƙasar Ivory Coast domin karfafa guiwar Super Eagles a fafatawar su da ƙasar Afirka ta Kudu a wasan dab da na ƙarshe.
Mai kula da ofishin yaɗa labarai na mataimakin shugaban ƙasar, Stanley Nkwocha, ne ya bayyana hakan a Abuja ranar Laraba.
- AFCON 2023: Gwamnonin APC Za Su Ba ‘Yan Wasan Super Eagles Kyautar Miliyan 200
- AFCON 2023: Ciwon Ciki Ka Iya Hana Osimhen Buga Wasan Gobe
Kamfanin Dillancin Labaran Nijeriya (NAN) ya ruwaito cewa Nijeriya za ta fafata da tawagar Afrika ta Kudu a yammacin yau Laraba.
Nkwocha, ya ce, zuwan Kashim Shettima kasar Ivory Coast, wani abu ne dai zai ƙarfafa gwiwar ƴan Nijeriya da suke je Ivory Coast domin goyawa Super Eagles baya, ba wai ƴan wasan kawai ba.
Ya ƙara da cewa tawagar Super Eagles na da tarin tairihi a gasar AFCON “wannan shi ne karo na 15 da Super Eagles ta kai irin wannan zagayen, kuma shi ne mafi yawan da wata kungiya ta taba kai wa a tarihin gasar” inji shi
Ya kuma yi kira ga ƴan Nijeriya da su goyawa tawagar ta Super Eagles baya da kuma musu fatan alhairi a wannan gasar.
A shekarar 2013 ce dai awagar Nijeriya ta lashe gasar cin kofin Afirka wanda ya gudana a ƙasar Afirka ta Kudu.