A kwanakin nan, kotun kasa da kasa na MDD ta yanke hukunci kan wasu bukatu dake kunshe a cikin karar da kasar Afirka ta Kudu ta shigar bisa zargin kasar Isra ‘ila da aikata kisan kare dangi a yankin Gaza, inda kotun ta umarci Isra’ila da ta kawo karshen duk wani mataki na kisan kiyashi, da daukar matakan sassauta yanayin jin kai a yankin Gaza. Daga baya, a nasa bangare, shugaban hukumar kungiyar kasashen Afirka AU, Moussa Faki Mahamat, ya bayyana farin cikinsa bisa hukuncin da kotun ta yanke, inda ya ce matakin ya kare kwarjinin dokokin kasa da kasa.
Game da yakin da ake yi a yankin Gaza, kasashen Afirka sun bukaci a kare fararen hula, da tsagaita bude wuta, ta yadda za a samu damar daidaita rikicin ta hanyar lumana bisa ka’idojin kasa da kasa. Wannan ra’ayi ya zama daya da na kasar Sin. Da ma yayin da ministan wajen kasar Sin Wang Yi ke ziyara a wasu kasashe 4 dake nahiyar Afirka a kwanakin baya, ya tattauna batun Falasdinu tare da bangarorin Masar da Tunisia, da kuma sakatariyar kungiyar kasashen Larabawa. A cewar Mista Wang, kasar Sin tana Allah wadai da duk wani matakin da zai lahanta fararen hula, da keta ka’idojin kasa da kasa, kana kasar tana goyon bayan yukurin magance tsanantar rikici, da neman dawo da zaman lafiya. Kamar dai yadda suke da ra’ayi daya dangane da yakin da ake yi tsakanin kasashen Rasha da Ukraine, kasar Sin da kasashen Afirka suna ci gaba da tsayawa kan wani bangare da zai tabbatar da zaman lafiya da adalci.
- Sharhi: Shin Isra’Ila Za Ta Yi Biyayya Ga Hukuncin Kotun Duniya Game Da Yakin Gaza?
- Bankunan Kasashen Ketare Sun Yaba Da Bunkasuwar Tattalin Arzikin Kasar Sin
A sa’i daya, kasar Amurka da wasu kawayenta na yammacin duniya sun yi na’am da matakan da kasar Isra’ila ta dauka na wai “kare kanta”, inda suka dinga samar da makamai da kudi ga bangaren Isra’ila, duk da cewa matakan sojojin Isra’ila sun riga sun haddasa asarar rayukan Falasdinawa fiye da 26,000, ciki har da yara fiye da 10,000, kuma Isra’ila ta kai hari kan asibitocin yankin Gaza, da neman lalata tsarin samar da abinci na yankin don haddasa yunwa a can, kuma tuni babban taron MDD ya zartas da kudurin tsagaita bude wuta a yankin Gaza bisa takardun amincewa guda 153 da kasashe daban daban suka jefa.
Ban da haka, wani abun da ya faru a kwanan nan shi ne, sakamakon yadda kasar Isra’ila ta zargi wasu ma’aikatan hukumar da ba da agaji ga ‘yan gudun hijira Falasdinawa ta MDD UNRWA da hannu a harin da aka kai Isra’ila, kasashe 10 da suka hada da Amurka, da Birtaniya, da Jamus, da dai sauransu, sun dakatar da samar da kudi ga hukumar, duk da cewa akwai mutane fiye da miliyan 2 a yankin Gaza da suke dogaro kan hukumar wajen samun kayayyakin rayuwa da suke bukata.
Yadda kasashen yamma suka karkata ga wani bangare maimakon nuna adalci, har ya fusata masanansu, inda Renad Mansour, mai nazarin harkokin yankin gabas ta tsakiya na cibiyar nazari ta Chatham ta kasar Birtaniya, ya rubuta wani labari a kwanan nan, cewa “Bayan da kotun duniya ta amince da ikon da take da shi na bin bahasin kasar Isra’ila kan yadda take aiwatar da kisan kare dangi a yankin Gaza, hakan ya yi kama da gurfanar da ‘tsare-tsaren duniya da aka kafa bisa wasu ka’idoji na tushe’ a gaban kuliya. ” A cewar Mista Mansour, cikin shekaru fiye da 10 da suka gabata, kasashen yamma su kan gudanar da matakan soja a duniya don kare moriyarsu, musamman ma a fannin siyasa, amma duk da haka suna fakewa da maganar “kare dimokuradiyya, da hakkin dan Adam, gami da ka’idojin kasa da kasa” don halatta ayyukansu. Sai dai a halin yanzu, mai kafa tsari yana bata tsari. Sakamakon yadda sojojin Isra’ila suke wa yankin Gaza zobe, da jefa dimbin boma-bomai a kan Fadasdinawa, ba za a ci gaba da yarda da maganar kasashen yamma, ta samun wani tsarin kasa da kasa da aka kafa bisa ka’idoji ba.
Hakika galibin kasashe ba su son yin biyayya ga kasashen da suke kokarin yin babakere a duniya, da dogaro kan wadanda ke da karfi. Maimakon haka, suna son ganin wani tsarin kasa da kasa mai adalci, wanda ya shafi bangarori da dama, da neman samun wani muhalli mai zaman lafiya da kwanciyar hankali da zai amfani ci gaban tattalin arziki. Wani abun da za a iya hanga yanzu shi ne, bisa rincabewar tsare-tsaren kasa da kasa da suka mai da kasashen yamma a matsayin jagora, tunani da murya da kasashen Afirka da kasar Sin suka gabatar za su taka muhimmiyar rawa a harkokin kasa da kasa, gami da samar da gudunmowa a kai a kai ga yunkurin kare zaman lafiya da adalci a duniya. (Bello Wang)