Ahmed Musa, sabon babban manajan ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Kano Pillars, ya fito ƙarara ya ƙaryata jita-jitar cewa ya raba motocin alfarma ga ‘yan wasan da jami’an kulob ɗin bayan karɓar sabon muƙaminsa.
Zargin ya samo asali ne daga wani saƙon da wani mai amfani da Facebook, Thomas Jeremiah Gora, ya wallafa wanda ke ɗauke da hotunan motocin Toyota Land Cruiser, yana iƙirarin cewa Musa ya bai wa kowanne ɗan wasa da jami’i motar a ranar farko da ya hau ofis.
- Zan Yi Ƙoƙarin Dawo Da Martabar Kano Pillars A Idon Duniya — Ahmed Musa
- Farfesa Haruna Musa Ya Lashe Zaɓen Shugabancin Jami’ar Bayero Ta Kano
Amma a wata sanarwa da aka fitar daga shalƙwatar kulob ɗin, Ahmed Musa ya bayyana labarin a matsayin “cikakken ƙarya,” yana mai buƙatar jama’a da kafafen yaɗa labarai su riƙa tabbatar da sahihancin bayanai kafin yaɗa su.
Musa ya jaddada cewa irin wannan labaran marasa tushe na iya jefa kulob ɗin cikin ruɗani da rushe martabar shugabanci. Ya kuma tabbatar wa da magoya baya da masu ruwa da tsaki cewa za su ci gaba da mayar da hankali wajen gina ƙungiya mai ƙarfi, da ladabi da nasara.
A matsayin sabon babban manaja, Musa ya buƙaci haɗin kai da goyon bayan kowa don tabbatar da gaskiya da amana a dukkan harkokin kulob ɗin. Ya kuma roƙi magoya bayan ƙungiyar su ci gaba da marawa kulob ɗin baya a wannan sabuwar tafiya ƙarƙashin jagorancinsa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp