Idan muka waiwayi juyin juya halin masana’antu guda uku na farko, wato muhimman karfin gudanar da ayyukan masana’antu kamar fasahar injuna, da fasahar laturoni da fasahar sadarwa duk sun ba da gudummawa matuka wajen gudanar da harkokin masana’antu daban-daban. A yau, kirkirarriyar basira ko fasahar kwaikwayon tunanin dan Adam wato AI, bisa matakin zurfafa kwaikwayon basira a manyan dandamalin kwanfutoci wanda ke ba da damar samar da fasahohin kirkire-kirkire yana habaka yadda masana’antu ke samar da hajoji da hidimomi masu karko cikin sauri da sauki kuma a farashi mai rahusa.
Tun bayan da aka kaddamar da yin sauye-sauye da bude kofa ga waje a shekarar 1978, bunkasuwar tattalin arzikin kasar Sin ya samu daukaka daga yin amfani da yawan jama’a da karfin tuwo wajen gudanar da ayyuka zuwa hada-hadar masana’antu bisa karfin fasahar zamani. Muna iya kafa misali da ikon samar da makamashi bisa hasken rana da sauran hanyoyin samar da makamashi maras gurbata muhalli, ga maganar masana’antar abeben hawa na sabbin makamashi, wadanda ke jagorantar ci gaban kiyaye muhalli na duniya.
- Xi Jinping Ya Gana Da Firaministan Hungary
- Kasar Sin Na Tunawa Da Kutsen Japan Tare Da Nanata Muhimmancin Neman Ci Gaba Cikin Lumana
A halin yanzu mun shiga zamanin tsananin gasa a fannin AI, kuma a matsayin muhimmin jigo na sabon karfin samar da hajoji da hidimomi masu karko, aikin habaka AI zai kawo ci gaba da juyin juya hali a bangaren inganta fasaha da kuma saukin aiki da ingancin hajoji, da sabbin kirkire-kirkire da kyautata tsarin gudanar da harkokin samar da hajoji da hidima, da zurfafa sauye-sauyen masana’antu daidai da bukatun zamani da habakawa. Duk da yanayin rashin tabbas da kalubale daga ketare, masana’antar AI ta kasar Sin tana da armashi da kyakkyawar makoma saboda tana da cikakkiyar tsarin kayan aiki na masana’antu, kama daga kwakwalen AI wato chips zuwa samfuran manyan jerin dokoki ko ka’idojin lissafi da warware matsaloli wato algorithms da manyan manhajoji, tare kuma da dimbin kwararrun injiniyoyi da wadataccen yanayin da tarin bayanai na aiki, wadanda suka zama tushen wadata a fannin samar da hajoji da hidimomi masu karko cikin sauri, kuma a farashi mai rahusa.
Bisa kididdigar da ma’aikatar masana’antu da fasahar sadarwa ta kasar Sin ta fitar, ya zuwa watan Yunin shekarar 2023, darajar babban ma’aunin ainihin masana’antun AI na kasar Sin ya kai yuan biliyan 500, kwatankwacin dalar Amurka biliyan 68.8, dauke da kamfanoni sama da 4,400 na AI.