A yau Talata, Zaɓaɓɓen gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya ƙaddamar da kwamitin karɓar mulki mai membobi 60, inda ya ƙara jaddada cewa ya zo aikin ceto ne tare da sake gina Zamfara.
Kwamitin mai membobi 60 a ƙarƙashin jagorancin tsohon Sufeto Janar na ‘yan sanda, M.D Abubakar, an kaddamar da shi ne a Gusau, babban birnin jihar.
Sanarwar manema labarai da ofishin zababben gwamnan ya fitar dauke da rattaba hannun, Sulaiman Bala Idris, ta bayyana cewa, da yake jawabi a wajen ƙaddamar da kwamitin, Dauda Lawal, ya ce nauyin da ya rataya a kan kwamitin shi ne gudanar da shirye-shiryen da suka dace domin karɓar mulki cikin kwanciyar hankali a jihar Zamfara.
Ya bayyana kwamitin mai membobi 60 a matsayin taron ƙwararru da ke da gogewar shekaru a ɓangarori daban-daban, waɗanda aka zaɓo su cikin tsanaki domin shiga cikin tsarin karɓar mulkin.
“Canjin da al’ummar Zamfara suka zaɓa, canji ne daga rashin tsaro, rayuwar talauci, zuwa rayuwa ta tsaro, wadata da walwala, riƙon amana, da mutunta doka.
“Kwamitin amsar mulkin mai membobi 60 an kafa shi ne da nufin fara dukkanin shirye-shiryen da ya kamata tare da kuma tsara yadda za a samu sauyi cikin sauƙi na sabuwar gwamnatinmu a jihar wanda zai fara aiki a ranar 29 ga Mayu, 2023.
“An ɗorawa kwamitin alhakin samar da ingantaccen tsarin haɗin gwiwa da samar da hanyar sadarwa ta yau da kullum da Gwamnati mai barin gado tare da kuma karɓar ragamar gudanarwar gwamnati mai zuwa domin samun nasarar karɓar mulkin.
“Kwamitin zai kuma haɗa hannu da ma’aikatu, rassa da kuma hukumomi, sannan zai duba kuɗaɗen gwamnati mai barin gado tare da mai da hankali kan rasiɗai, ƙadarori, da kuma lamuni da sauransu.
“Al’ummar jihar Zamfara na da kyakkyawan fata; sun zaɓe mu ne cike da imanin za mu iya ceto tare da sake gina jiharmu.
“Mun kuma zaɓe ku a matsayin membobin kwamitin karɓar mulki saboda mun yi imanin cewa tsawon shekarun gogewarku da ƙwarewar ku, za mu iya aza harsashi ga gwamnati mai jiran gado domin ta yi nasara kan aikin ceton da ta sa gaba.
“Da wannan taƙaitaccen bayani da kuma yardar Allah, a halin yanzu, nake ƙaddamar da wannan kwamitin na karɓar mulki.”
A ranar 29 ga Mayun 2023 ne ake sa ran rantsar da sabon zababben gwamnan a Gusau babban birnin Jihar Zamfara.