Kungiyar dalibai ta kasa (NANS) ta yi Allah-wadai da tsare Aminu Adamu bisa zargin rubutun cin zarafi da yayi kan uwargidan shugaban kasa, Aisha Buhari a shafin sada zumunta a manhajar Twitter.
Shugaban NANS, Usman Barambu, a wata sanarwa a ranar Alhamis da ya fitar, ya bukaci a sako dalibin jami’ar tarayya dake Dutse, jihar Jigawa ba tare da wani bata lokaci ba.
Ya kuma sanar da shirin gudanar da zanga-zanga a fadin kasar a ranar Litinin, 5 ga Disamba, 2022 don matsa lamba ga hukumomin da abin ya shafa a sako Dalibin, Aminu.
Sanarwar ta ci gaba da cewa, “Bayan yin iya kokarin mu kan kokarin ganin an sako mambanmu wanda aka tsare ta hanyar da ta dace ba, da azabtarwa, cin zarafi da kuma tsare shi daga jami’an gwamnati.
“Muna sanar da ku matakin da shugabannin kungiyar dalibai ta kasa ta dauka na gudanar da zanga-zanga a fadin kasar baki daya,” in ji shugaban NANS a wata sanarwa da ya aikewa sassan kungiyar.