Jiya Litinin ne sakataren harkokin wajen kasar Amurka Antony J. Blinken ya kammala ziyararsa ta kwanaki 2 a kasar Sin. A lokacin ziyarar tasa, shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya gana da shi, yayin da manyan jami’an kula da harkokin diplomasiyya na kasar suka yi shawarwari da shi, inda bangarorin 2 suka amince da aiwatar da ra’ayi daya da shugabannin kasashen 2 suka cimma, a taronsu na tsibirin Bali, lamarin da ya sanya tagomashi ga kyautatuwar hulda a tsakanin kasashen 2.
A yayin ziyarar Blinken, kasar Sin ta nuna cewa, yanzu haka hulda a tsakanin kasashen Sin da Amurka ta yi tsami, saboda Amurka ba ta fahimci kasar Sin daidai ba, ta kuma aiwatar da manufofi marasa dacewa kan kasar Sin. Don haka wajibi ne Amurka ta yi tunani sosai. Amurka ta dade tana mayar da kasar Sin babbar abokiyar takararta, da yi mata barazana mafi muni cikin dogon lokaci. Don haka tana aiwatar da manufofi marasa ma’ana, kuma masu sabawa juna kan kasar Sin.
Huldar dake tsakanin kasashen 2, hulda ce mafi muhimmanci a duniya, wadda ke shafar makomar dan Adam baki daya. Don haka ya wajaba sassan biyu su yi hangen nesa, wajen raya huldarsu ba tare da wata matsala ba.
Hakan ya sa abu mafi muhimmanci shi ne bin ka’idojin da shugaba Xi Jinping ya gabatar, wato mutunta juna, da zaman tare cikin lumana, da hada kai domin samun nasara tare.
A ciki kuma, batun Taiwan ya fi muhimmanci ga kasar Sin, wanda shi ne matsalar da ta fi muni a huldar dake tsakanin kasashen 2. Ban da haka kuma, kasar Sin ta bukaci Amurka ta dakatar da baza kalaman wai “kasar Sin barazana ce”. Wajibi ne ta soke takunkumin kashin kai da ta sanya wa kasar Sin ba bisa doka ba, ta kuma dakatar da danne ci gaban kimiyya da fasahar kasar Sin. (Tasallah Yuan)