Shugaban Asibitin Dalhatu Araf (Specialist Hospital) Dr. Ikrama Hasan ya bayyana cewa cigaba ne samar da asibitin koyarwa na tarayya a jihar, hakan na zuwa a lokacin da yake zantawa da wakilinmu jim kaɗan bayan mika takardan tabbatar da Asibitin a garin Lafia.
Dr. Ikrama yace, cancanta aka duba saboda Jami’ar Gwamnatin tarayya tana garin lafia ne, kuma dalubai da za a rika koyar da su suna garin lafia ne su ma, kuma nan ne gurbin da ya cancanta a ajiye Asibitin saboda kusanci.
- Jirgin Ruwan Sin Mai Dauke Da Asibitin Tafi Da Gidanka Ya Kammala Aiki A Mozambique
- An Tona Asirin Ainihin Dalilin Saukar Hadimin Tinubu
Yace, Asibitin zai riƙa koyar da ɗalibai masu koyon aikin kiwon lafiya kuma za a riƙa kula da marasa lafiya a Asibitin. Kana za a kawo wadatattun kayan aiki da ma’aikatan da zasu riƙa kula da marasa lafiya.
Ya ƙara da cewa ajiye Asibitin Dalhatu Araf ( Specialist Hospital) a garin Akwanga wannan abin a yabawa Gwamnan jihar Nasarawa ne, saboda yayi abin a yaba.
Mutanen da ke rayuwa a yankin Akwanga zasu samu kusanci da babban Asibiti kusa da su.
Daga Zubairu M Lawal Lafia
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp