Shugaba Bola Tinubu ya bai wa Shugaban Majalisar Dattawa Godswill Akpabio, Babbar Alkalin Alkalan Nijeriya (CJN) Kudirat Kekere-Ekun, da Kakakin Majalisar Wakilai, Tajudeen Abbas lambar girmamawa ta kasa.
Tinubu ya bayyana wannan a cikin jawabin da ya yi wa kasa a safiyar Talata don bikin cikar Nijeriya shekaru 64 da samun ‘yancin kai.
- NUJ Ta Taya Gwamnan Kebbi Da Nijeriya Murnar Cika Shekaru 64 Da Samun ‘Yancin Kai
- MƊD Ta Ƙaddamar Da Shirin “Muryoyi Daga Sahel” Karo Na Biyu
Sauran wadanda suka samu wannan lambar girmamawa sun hada da Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa Barau Jibrin da Mataimakin Kakakin Majalisar Wakilai, Benjamin Kalu.
Ya ce hakan na da nasaba da mukamansu masu muhimmanci a bangaren majalisa da bangaren shari’a.
Shugaban kasa ya kuma ce nan ba da jimawa ba za a sanar da sunayen sauran wadanda za su samu lambar girmamawa ta kasa ta 2024.
“An bai wa Shugaban Majalisar Dattawa da Babbar Alkalin Alkalan Nijeriya lambar girmamawa ta Grand Commander of the Order of the Niger (GCON).
“Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa da Kakakin Majalisar Wakilai sun samu lambar Commander of the Order of the Federal Republic (CFR), yayin da Mataimakin Kakakin Majalisar Wakilai ya samu lambar Commander of the Order of Niger (CON),” in ji Tinubu.