Shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, ya dawo daga gajeriyar hutu da ya tafi Landan, inda ya ƙaryata jita-jitar da ke cewa yana fama rashin lafiya kuma an kwantar da shi a asibiti a Birtaniya.
Kafin ya tafi hutun, Akpabio ya halarci taron shugabannin majalisun dokoki na duniya da aka gudanar a Geneva daga 29 zuwa 31 ga watan Yuli, 2025.
- Dole Ne A Nace Kan Manufar Sin Daya Tak Don Kiyaye Zaman Lafiya A Mashigin Taiwan
- Kudin Kallon Fina-Finai Da Aka Samu A Lokacin Zafi Na 2025 A Sin Ya Zarce Yuan Biliyan 10
Ya sauka a filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja da misalin ƙarfe 4 na asubar ranar Litinin, inda sanatoci, hadimai da magoya baya suka tarbe shi.
Da yake magana da ’yan jarida bayan dawowarsa, Akpabio ya ce yana cikin ƙoshin lafiya kuma zai ci gaba da aiki tuƙuru.
“Babu gaskiya a cikin wannan magana. Ina cikin ƙoshin lafiya. Na tsaya ne kawai a Landan domin yin ɗan gajeren hutu,” in ji shi.
Ya kuma yi alƙawarin cewa majalisar dattawa za ta yi aiki yadda ya kamata idan ta dawo daga hutu.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp