Shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, ya bayyana sunayen wadanda aka nada a manyan mukamai na majalisar dattawa ta 10.
Daga cikin wadanda aka nada sun hada da Sanata Opeyemi Bamidele a matsayin shugaban masu rinjaye na majalisar dattawa.
- Mutanen Da Ke Aiki A Karkashina Na Da Gidaje A Kasashen Waje, Amma Ba Ni Da Gida A Waje -Dangote
- Dalilin Da Ya Sa Nake Shiga Sha’anin Gwamnatin Kano -Kwankwaso
Bamidele na wakiltar Ekiti ta Tsakiya a majalisar dattawa.
Sauran sun hada da Sanata David Umahi mai wakiltar Ebonyi ta Kudu a matsayin mataimakin shugaban masu rinjaye.
Tsohon Shugaban Masu Rinjaye a Majalisar Dattawa ta 8, Sanata Mohammed Ali Ndume, mai wakiltar Borno ta Kudu, shi ne mai tsawatarwa a majalisar dattawa, yayin da Sanata Lola Ashiru, mai wakiltar Kwara ta Kudu a matsayin mataimakin mai tsawatarwa.
Akpabio ya ce an nada su a mukaman ne bisa yarjejeniya.