Tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasiru El-Rufai, ya bayyana cewa sauyin jam’iyyar da manyan ‘yan suke yi zuwa jam’iyyar APC ana kamba ma shi fiye da yadda ya kamata, yana cewa wannan sauyin ba zai shafi kokarinsa na neman mafita ga matsalolin Nijeriya ba. Ya bayyana hakan ne yayin ganawarsa da manema labarai a Kano yau Litinin.
El-Rufai ya bayyana cewa shi ne na farko da ya koma jam’iyyar Social Democratic Party (SDP) daga APC a kokarinsa na warware matsalolin Nijeriya ta hanyar kawar da tsarin kawancen siyasa.
- Ficewar El-Rufai Daga APC Babban Rashi Ne – Tsohon Hadimin Buhari
- El-Rufai Ya Shiga Tsilla-tsilla Bayan Rasa Kujerar Minista – APC
“SDP ta hankali wajen nemo mafita ga matsalolin Nijeriya da kuma ba da dama ga wadanda a siyasance ta hanyar kawancen jam’iyyu” in ji El-Rufai.
Ya kara da cewa sauyin jam’iyyar ‘yan siyasa ba shi ne babban batu ba, a cewarsa, babban batu shi ne wanda zai iya warware matsalolin Nijeriya da kuma isar da wannan ga al’umma ta yadda za su fita zabe a ranar zabe.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp