Bayan da sabon kociyan na Manchester United, Erik ten Hag, ya fara buga wasa da qafar hagu, masana harkokin wasanni sun bayyana cewa akwai gagarumin aiki a gaban kociyan, xan asalin qasar Holland.
Manchester United ta sha kashi a hannun qungiyar Brighton da ci 2-1 har filin wasanta na Old Trafford a wasan farko da fara Premier League ta bana bayan da Brighton ta fara cin qwallo ta hannun Pascal Gross saura minti 15 su yi hutu, sannan shi ne ya qara ta biyu a minti tara tsakani.
- Salman Rushdie: Wanda Ya Yi Batanci Ga Annabi Na Cikin Mawuyacin Hali Bayan Kai Masa Hari
- Wike Ga Atiku : Kar Ka Zarge Ni In Ka Fadi A Zabe
Kawo yanzu Pascal Gross ya ci Manchester United qwallo shida a Premier League shi kaxai – shi ne kan gaba xan wasan Brighton da ya ci Manchester Uniteed qwallaye da yawa a gasar firimiyar Ingila.
Manchester United ta zare qwallo xaya bayan da aka koma zagaye na biyu, bayan da Alexis Mac Allister ya ci gida, saura minti 22 a tashi daga wasan kuma karon farko da qungiyoyin suka buga wasan buxe Premier League wato makon farko a tsakaninsu.
A kakar da ta wuce, Brighton ta doke Manchester United 4-0 ranar 7 ga watan Mayu, bayan da tun farko United ta ci Brighton 2-0 ranar 15 ga watan Fabrairun shekara ta 2021, sannan a wasa 14 baya kan haxuwar ranar Lahadi.
Brighton ta yi rashin nasara a wasa 12 a Old Trafford har da kwasar kashi a karawa takwas a jere a gidan United.
Koci biyar ‘yan qasar Netherlands da suka fara jan ragamar wasan farko a Premier sun sha kashi, in ban da Guus Hiddink a Chelsea da ta doke Aston Villa a Villa Park a Fabrairun 20009 kuma United ta xauki wasu sabbin ‘yan wasa don tunkarar kakar bana da ya haxa da Tyrell Malacia daga Feyenoord da Christian Eriksen, wanda yarjejeniyarsa ta qare a Brentford da kuma Lisandro Matinez daga Ajax.