Gwamnatin Jihar Kano ta amince da nadin shugabannin gudanarwa da mambobi 20 na hukumar shari’ar musulunci ta Jihar Kano.
Kwamishinan yada labaran Jihar Kano, Malam Muhammad Garba shi ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da daraktan ayyuka na musamman na Jihar Kano, Sani Abba Yola ya fitar a ranar Alhamis.
- Masarautar Mubi Da Kyakkyawan Shugabancin Sarki Alhaji Abubakar Isa Ahmadu
- 2023: Ko Yawan Masu Rajistar Zabe Zai Iya Tasiri Ga ‘Yan Takara?
Sanarwa ta ce amincewar ta biyo bayan shawarar kwamitin da aka kafa domin duba ayyukan hukumar kan dacewa da tanadin dokar jihar.
Ya ce rahoton kwamitin ya ba da shawarar kafa kwamitin gudanarwar, sannan kuma majalisar dokokin jihar ta amince da shi.
Malam Garba ya bayyana cewa an zabo mambobin kwamitin ne bisa la’akari da iya aiki da cancantar su.
Kwamishinan ya ce daga cikin kwamitin akwai, Sheikh Muhammad Nasir Adam a matsayin shugaban zartarwa tare da Sheikh Jamilu Abubakar da Sheikh Abdulkadir A. Ramadan a matsayin kwamishina na daya da kwamishina na biyu.
Ya kara da cewa mambobin sun hada da Sheikh Abdulwahab Abdallah a matsayin shugaba; Sheikh Bashir Aliyu, Sheikh Umar Sani Fagge, Sheikh Ibrahim Maibushira, Uztaz Muhammad Al-bakari a matsayin membobin, yayin da Dakta Muhammad Tahar Adamu, kwamishinan harkokin addini na jiha zai kasance sakataren hukumar.