Sarkin Fawan Jiwape, Abdullahi ya yi kira da shugabannin Arewa su farka daga barcin da ya dauke su, saboda akwai abubuwan da suka addabi yankin Arewa, amma sun nunakamar abin ba ya damunsu.
Sarkin ya yi wannan magana ne lokacin da yake hira da manema labarai a Jiwape, ya ce hakika lamarin yana matukar ci mai tuwo a kwarya, domin kuwa sashen Arewa a shekarun da suka gabata abun gwanin ban sha’awa, amma yanzu sai dai a yi hakuri.
- NNPCL Ya Tabka Babban Kuskure Bisa Rage Hannun Jarinsa A Matatarmu – Dangote
- Mutane 9 Sun Rasu Sakamakon Kamuwa Da Cutar Kwalara A Yobe
Ya yi kira da shugabnnin su kara hade kansu su manta da duk wani lamarin da su-ka san zai kara rarraba kansu, saboda sai an samu hadin kai sannan a yi tunanin samun wani ci gaba.
Daga karshe, ya yi kira da ‘yan majalisu su rika yin dokokin da za su amfanar al’ummar da suka zabe su da kuma kasa baki daya.