• English
  • Business News
Monday, October 13, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Akwai Kalubale Ga Matan Da Ba Su Da Sana’a – Aisha Isah

by Rabi'at Sidi Bala
3 years ago
Aisha

Hausawa na cewa sana’a jari ce, ya yin da matashiya mai sana’ar girke-girke Aisha Isah Sulaiman, wadda aka fi sani da (Nerhnerhs Pastries And More) ta bayyana irin kalubalen da take fuskanta wajen kostamominta, ta kuma yi jan hankali ga mata na gida musamman marasa aikin yi har ma da wasu batutuwan da suka shafi sana’arta. Ga dai tattaunawar tare da wakiliyarmu RABI’AT SIDI BALA kamar haka;

Masu karatu za su so jin cikakken sunanki da kuma sunan da aka fi saninki da shi?

Da farko dai ni sunana Aisha Isah Suleiman, amma an fi sanina da ‘Nernerhs Pastries And More’.

Ko za ki fada wa masu karatu dan takitaccen tarihinki?

To ni dai haifaffiyar garin Bauchi ce, a Bauchi aka haife ni a nan na girma har na yi aure. Na yi ‘Nursery da Firamarena a ‘Fomwan Nursery and Primary School’, sannan koma ‘Fomwan Model Secondary School’ inda a nan na gama ‘Sikandire’, daga nan na tafi Jami’ar Bauchi Gadau inda nake karanta ‘English and literary studies’.

LABARAI MASU NASABA

Gwamna Dauda Lawal A Shekara 60: Inda Akwai Fata, Akwai Mafita

GORON JUMA’A

Sannan kuma Ina kasuwancina ‘Baking and Catering Serbices’, wanda na fara wannan kasuwancin ne tun 2016 kuma na yi aure 2021, a taikace wannan shi ne abin da zan iya cewa.

Me ya ja hankalinki har kika fara wannan sana’a?

Aisha
Tun tashina masu irin sana’ar abinci da kayan fulawa suke birge ni, kuma nake son abin a raina wanda na yi addu’a Allah ya cika min burina nima na zama daya daga cikin irin mutanen, kuma Alhamdulillah ina irin sana’ar nima.

Lokacin da za ki fara ita wannan sana’ar, shin kina sarowa ne sai ki sayar ko kuwa da kanki kike zama ki yi kamar abin da ya shafi kayan fulawar?

A’a ba na sara gaskiya, na tashi mahaifiyata tana irin sana’ar itama ana kawo mata aikin biki ko suna da sauran abubuwa, to a nan nake gani har na shiga makarantar koyon abinci kuma mahaifiya ta ta ci gaba da koya min a gida, bayan na iya abin har na fara yi mana a gida na zo na fara talla nima wajen mutane, to shi ne har Allah ya bani kuwa na fara na kudi nima.

Bayan wannan sana’ar akwai wata sana’ar da kike yi ne, kamar da me da me kike sayarwa?

Ina sana’o’i guda uku ne gaskiya, iya ‘Baking and pastries, Catering serbices, Natural drinks’, nake yi.

Za ki yi kamar shekara nawa kina yin sana’o’in?

Shekara hudu, na kai shekara shida ina yi, amma a shekara hudu ne gaskiya na samu har ake bani aiki sosai.

Idan na fahimce ki kina so ki ce a yanzu har kwangila ake baki kenan?

Eh! sosai ana bani kwangila.

Ya gwagwarmayar kasuwancin ta kasance musamman farkon farawarki?

Gaskiya na yi fuskanci kalubale iri-iri musamman Lokacin da na fara abin ban gama sanin kansa ba, wani lokaci zan yi abu bai yi kyau ba wani lokaci kuma na yi asarar abin kai wani lokaci har na fara karaya akan an ya ba zan hakura da wannan kasuwancin ba kuwa, haka dai na yi tafiya sai kuma kalubalen da nake fuskanta wajen Kwastomomi wani ya zage ka wani ya bata maka rai, wasu ma su fada maka abin da suka ga dama amma haka muka yi tafiya.

Game da sana’ar da nake yi kuma na yi ta kokarin gyara abu domin ina abu mai kyau da inganci wa mutane kuma Alhamdulillah Allah ya ci gaba da taimaka na har abubuwa suka zama dai-dai sai ‘yan kananan kusakurai da ba a rasa wa a kasuwanci sai kuma kalubale daga wajen mutane jifa-fifa.

Shin akwai wani waje ne na musamman da kika ware har kike gabatar da sana’o’inki ko kuwa duk a gida kike yin su?

Eh ‘Natural drinks’ ‘supermarket’ nake kai wa, sauran kuma a gida nake yi.

Taya kike iya bunkasa kasuwancinki?

Eh to gaskiya na je kasuwar zamani ne na nemi manaja, na ce masa ina ‘natural drinks’ ne ga samfuri na kawo musu su yi dandana sai su bani sakamako tun da akwai bayanaina a jikin kwalbar.

Alhamdulillah Allah ya taimaka suka kira ni suka ce na kawo musu Katan biyu su gwada daga nan shikenan sai suka fara karba a sari ina kai musu da abu ya yi ta tafiya har Allah ya bani ikon sayen firji na kai musu idan na yi kayan sha zakina. Sai na je na cika firji da shi tun da ko da yaushe suna da wuta daga nan abu ya yi ta bunkasa har na kawo inda nake, kuma da taimakon mijina saboda shi ya yi ta kwarin gwiwa gaskiya sosai a kan kasuwancina da nake yi.

Kamar wanne irin kalubale kika taba fuskanta game da sana’ar ki wanda ba za ki taba iya mantawa da shi ba?

Eh to babban kalubalen da nake fuskanta wanda kuma ba zan iya mantawa da shi ba shi ne daga wajen kwastomomi, irin yadda wasu suke maka abu da gadara saboda akwai wacce ta taba zagi na uwa da uba amma ban ce mata komai ba saboda na yi mata aiki za ta kawo min kudi sai ta dauki abin to bata biya ni ba nace dole sai ta biya kafin na bata to shi ne ta rinka zagi na. Toh gaskiya ba zan taba mantawa da irin ta ba, sai kuma wajen abokan kasuwanci dinka wani a fili zai gwada maka yana jin haushin abin da kake samu ko yadda kasuwancin ka yake bunkasa to gaskiya ba zan manta da irin wannan kalubalen ba.

To ya batun Nasarori fa?

Aisha
Gaskiya nasara kam Alhamdulillah, saboda kasuwanci yana bunkasa sosai kuma ina ganin alkhairi sosai a cikinsa sai dai dama kasuwanci akwai riba akwai faduwa. To gaskiya ni dai a yanzu ban da abin da zan ce sai godiya ga Allah game da irin nasara da ci gaba da nake samu, saboda a nasarar da na samu ‘natural drinks’ da nake yi ‘supermarket’ nake kai wa, kuma ko wanne a cikin biyun da nake kai wa ina da firinji na babba a wajen su, ‘catering serbices’ kuma ina da duk wani kayan aiki na, haka zalika ‘baking and pastries’ duk wasu kayan aikina amfani ina da shi.

Yanzu misali idan wata na son koyan ita wannan sana’a ta ya za ta fara,wanne abubuwa za ta tanada?

Ya danganta da abin da take so ta koya, kai tsaye kin ga ba za ta ce za ta fara abu ba dole sai ta je ta koya sai ta zo ta fara sayen kayan aiki kuma a hankali har ta mallaki abubuwan da take so.

Idan mutum na son koya ta yaya zai iya saminki?

Zai iya samu na a ‘handle’ di na na ‘social media’ ko ya kira ni kai tsaye ma, ya yi min DM kawai.

Ko akwai wadanda kike koya wa ko kike burin koya musu?

Eh sosai akwai wanda na koya musu, kuma ina da burin na ci gaba da koyar wa mutane domin suma su dogara da kansu.

Me kike son cimma game da wannan sana’a taki?

Eh to, gaskiya ina so na bunkasa, kuma ina so in ga na bude ‘bakery’ da babban ‘restaurant’ in sha Allah da sauransu ina so na gina masallaci da kuma tona rijiyoyi.

Wanne kira za ki ga sauran mata na gida musamman marasa aikin yi?

Gaskiya su tashi su nemi sana’ar dogaro da kai saboda rayuwar yanzu ta zama da tsada kuma zama ba abun yi bai yi ba, gaskiya su tashi su nemi abin yi suma, domin akwai kalubale ga matan da basu sana’a.

Idan kika ga mata marasa sana’a ya kike ji cikin ranki?

Wallahi ji nake yi kamar ni ce a yadda suke, saboda tausayi suke bani wallahi har cikin raina nake jin ‘pain’ din.

Ko akwai wani kira da za ki ga gwamnati musamman game da bunkasa kasuwanci irin naku?

Eh! gaskiya idan gwamnati tana da hali masu karamin jari za su iya kara musu, su tallafa musu marasa jari ma za a iya basu domin su fara idan har halin haka ya samu ko da bashi ne kuwa.

Wacce shawara za ki bawa sauran abokan kasuwanci?

Abokan kasuwanci su ji tsoron Allah suna abu mai kyau da inganci saboda abu mai kyau shi yake tallata kansa kuma su cire kyashi da hassada a ransu don Allah.

Wanne irin abinci da abin sha kika fi so?

Gaskiya ina son shinkafa da mai da ya ji sosai shi ne abincin da na fi so, sai kuma ina son zobo.

Wanne irin kaya kika fi son sakawa?
A baya ko duguwa.

Me za ki ce da makaranta wannan shafi?

Gaskiya ba abin da zan ce musu sai dai na ce su ci gaba da kasancewa tare da wannan jarida mai albarka, masu shafin ma Allah ya saka da alkhairi game da irin abubuwan da suke yi na ci gaba da kuma na alkhairi.

Me za ki ce da ita kanta Jaridar LEADERSHIP HAUSA?

Gaskiya suna kokari yadda suke abubuwa da tsari kuma yadda ya kamata.

Ko kina da wadanda za ki gaisar?

Eh to! babban sakon gaisuwa ta zuwa wajen Anti Rabi’a wadda ta yi hira da ni, na ji dadi sosai yadda ta yi min komai cikin mutuntawa Allah ya saka da alkhairi sai kuma sakon gaisuwata zuwa wajen abokan aikinta.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Gwamna Dauda Lawal A Shekara 60: Inda Akwai Fata, Akwai Mafita
Al'adu

Gwamna Dauda Lawal A Shekara 60: Inda Akwai Fata, Akwai Mafita

September 2, 2025
GORON JUMA’A
Goron Juma'a

GORON JUMA’A

August 15, 2025
GORON JUMA’A 8-8-2025
Goron Juma'a

GORON JUMA’A 8-8-2025

August 8, 2025
Next Post
Mun Dakile Hari A Kano Da Ka Iya Zama Mafi Muni A Tarihin Nijeriya —Irabor

Mun Dakile Hari A Kano Da Ka Iya Zama Mafi Muni A Tarihin Nijeriya —Irabor

LABARAI MASU NASABA

Gwamnatin Tarayya Ta Ƙaddamar Da Gangamin Wayar Da Kai Kan Laifuka A Intanet

Gwamnatin Tarayya Ta Ƙaddamar Da Gangamin Wayar Da Kai Kan Laifuka A Intanet

October 13, 2025
Ana Gudanar Da Taron Masu Mukamin Magajin Gari Na Kasa Da Kasa A Birnin Dunhuang Na Sin

Ana Gudanar Da Taron Masu Mukamin Magajin Gari Na Kasa Da Kasa A Birnin Dunhuang Na Sin

October 13, 2025
Hukumar Kwastam Ta Tara Naira Biliyan ₦658.6 A Watan Satumba — DG Na NOA

Hukumar Kwastam Ta Tara Naira Biliyan ₦658.6 A Watan Satumba — DG Na NOA

October 13, 2025
Barazanar Amurka Ta Kara Haraji Game Da Batun Ma’adanan Farin Karfe Ba Hanya Ce Mai Bullewa Ba

Barazanar Amurka Ta Kara Haraji Game Da Batun Ma’adanan Farin Karfe Ba Hanya Ce Mai Bullewa Ba

October 13, 2025
Zargin Batanci: An Sasanta Da Malam Lawal Triumph Da Majalisar Shura Ta Kano

Zargin Batanci: An Sasanta Da Malam Lawal Triumph Da Majalisar Shura Ta Kano

October 13, 2025
Hada-Hadar Cinikayyar Waje Ta Sin Ta Karu Da Kaso 4% Cikin Watanni Tara Na Farkon Bana

Hada-Hadar Cinikayyar Waje Ta Sin Ta Karu Da Kaso 4% Cikin Watanni Tara Na Farkon Bana

October 13, 2025
Rundunar Ƴansanda Ta Kama Gaggan Ƴan Fashi 9 A Kano

Rundunar Ƴansanda Ta Kama Gaggan Ƴan Fashi 9 A Kano

October 13, 2025
Magance Bala’o’i: Gwamna Lawal Ya Jaddada Ƙudirin Gwamnatin Zamfara Na Ci Gaba Da Haɗin Gwiwa Da NEMA

Magance Bala’o’i: Gwamna Lawal Ya Jaddada Ƙudirin Gwamnatin Zamfara Na Ci Gaba Da Haɗin Gwiwa Da NEMA

October 13, 2025
Asuu

Ba Bu Dalilin Da ASUU Za Ta Fara Yajin Aiki, An Biya Duk Buƙatunsu – Ministan Ilimi 

October 13, 2025
hisba

Hukumar Hisbah Ta Kama Wasu Matasa Da Suka Yi Aure Ba Bisa Ƙa’ida Ba A Kano

October 13, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.