Wannan hira ce da shugaban Hadaddiyar Ƙungiyar ‘yan kasuwa ta Nijeriya, Dakta Bature Abdul’aziz dangane da zantukan da Amurka ta yi na cewa za a kawo hari babban birnin tarayya, Abuja.
Me za ka ce dangane da batun kai hari Abuja da Amurka ta yi?
Gaskiya ne idan ka ji labari mai daɗi ne ko mara daɗi, musamman mara daɗi ka ce ga wani abu nan ya taho. Da farko ka yi addu’a ko ya zo Allah ya sa kada ya yi tasiri, na biyu kuma ka shirya, in akwai jama’a da suke maƙotanka ka gaya musu a ci gaba da addu’a kuma a sa ido irin na tsaro.
Babu shakka wannan magana da Amurka suka faɗa, magana ce mai harshen damo. Wani harshen sai ka ga ya gani ɗin wataƙila wani abin zai faru, wani harshen kuma tsari ne na siyasar duniya, wani lokacin za ka ji ƙasashen nan manya da suka ci gaba idan suna jin haushin ƙasa za ka ji sun faɗi wani abin don a tashi a yi addu’a da komai da komai, wani abin kuma suna faza don su karya alƙadari da mutuncin ƙasa don a ga kamar ƙasa tana cikin wani mugun yanayi.
Gaskiya ne, domin yadda ƙasar take ciki a halin yanzu in wani ya ce wani abu zai faru, kada a jefar da zance a yi sauri a ɗauki mataki. Amma ni a ganina su a halin da suke ciki musamman ita Burtaniya, daga sanda ta fita daga Ƙungiyar Tarayyar Turai da ba a fi shekara biyu ba zuwa uku, a shekara biyun nan zuwa uku abin da ya samu Burtaniya sun canja shugaba huɗu kenan, wannan da gani ka san sharrinsu ne yake komawa kansu, ka san shi sharri ɗan aike ne inda duk ka aike shi za ka ga ya dawo.
Abin da ya sanyo Burtaniya gaba a yanzu mu da su, mu su yi mana addu’ar Allah ya kare mu, mu ma mu yi musu addu’ar Allah ya kare su, ko ba komai Burtaniya ai uwargijiyarmu ce, ma’ana ita ce ta yi mana mulkin mallaka, idan zance ta faɗa na alheri, to dama muna zaton za ata faɗi zance na alheri kan Nijeriya, in kuma akasin hakan take faɗa mu dai muna yi musu addu’a, amma irin waɗannan maganganun na firgita ƙasa ai dama sun saba yi, kuma sun sha faɗa har sau uku cewa Nijeriya za ta rabe biyu ga waɗanda suke kai musu labarin za su raba biyun, amma wanda ya haɗa tan Allah ne ya haɗa, Allah kuma ba zai raba ta ba darajar addu’a da ake yi kullum.
Ko akwai ƙarin bayani kan wannan?
Abubuwan da suka samu ƙasar Ingila a yanzu ka ga dai idan ka kwatanta da wancan kuɗi da wancan kuɗi, wannan kuɗi a da Fam ɗaya sai ka sa Dala da Santi 60 take a matsayin Fam ɗaya. A wancan makon da ya gabata ko wannan da muke ciki, sai da Fan ya dawo Dala ɗaya da Santi ɗaya, ka ga ta zubar da ‘One Teɗ’ na kuɗin gabaki ɗaya ma’ana kashi 35 ko da uku ya faɗi cikin ‘yan wanni kaɗan.
To ba ma yi wa Ingila mugun fata kullum muna ganin ta da girmamawa, to amma suma muna son shugabanninsu da suke zuwa daban-daban su riƙa tunawa mu amanarsu ce kuma duk da ƙarfi da yaji suka shigo mana, to har gobe muna yi musu fata alheri, musamman Mai Girma Sarauniyar Ingila da muka rasa ta.
To amma fa abin da ya sanyo su a gaba shi ne irin wannan hasashen nasu na rashin alheri, hasashen da ke zama na mugunta.
Amerika da Ingila su suka haɗu suka kunna wutar faɗan nan na Rasha da Yukiren, kuna ganin dai yadda faɗan Rasha Yukiren yake zama, kuma sanda faɗan ya fara suna ruwan da za su kashe wutar, amma dai babban ƙoƙarinsu shi ne kawai su ga rigimar nan da ake yi ta ci gaba, duk da suna ganin cewa kafin rigimar ta kai ga ƙarshe in dai ba Allah ne ya taƙaita ta ba ilahirin Yukiren kusan duk wani abu mai daraja an ragargaza shi.
Kamar yadda ku ke gani a hayaniyar tasu duk wuraren da suke Fizi rasha ta janye, amma duk inda suka san Nukiyar Rasha yake a Yukiren kafin a raba su sanda suna Tarayyar Soviet yanzu waɗannan wuraren suna hannun Rasha. Kuma waɗannan makaman na Nukiliyar su Turawan Yamma ke kwaɗayi, suna kwaɗayin sanda duk Yukiren ta dawo ƙuniyar Tarayyar Turai waɗannan Nukiyar da suke Yukiren waɗanda asalinsu na Rasha ne tun suna Tarayyar Soviet, in har Yukiren ta dawo Tarayyar Turai, to duk waɗancan makami masu ƙarfi sun dawo ƙarƙashin Tarayyyar Turai, saboda su Turai sun waɗannan makamai duk ta yi saitinsu ne kan manyan biranen Rasha, shi ya sa suke ƙoƙarin duk yadda za a yi su dawo da waɗacan makamai ɓangaren Yukiren.
Hakan abu ne mai wahala, domin bayan ma ba za su iya dawp waɗancan makamai inda suke nufi ba, ana daɗa cutar da Yukiren yadda kafin ta dawo dai-dai sai an shekara 20. Amma da yake shi matashi ne, wani lokaci bai san ya gaji ba har sai gajiyar ta kai shi ƙasa.
To muna fatan Ingila, irin wannan mummunan tunani da ya ja suka fita daga Tarayyar Turai, muna basu shawara da su koma Tarayyar Turai in ba haka ba, to Ingila ta kama hanyar da sai ta faɗi har ƙasa, amma ba ma fata.
Sai kuma Amurka, Amurka wannan bayanai da suke yi na wannan abu, to muna yi musu godiya, suma Amurka ƙawayen Nijeriya ne, kuma muna jin daɗi ƙawance da su, amma wani lokacin suna zama fuska biyu. Wani lokacin za ka ga fuskarsu fara tas, suna duban Afirka da ita, sau da yawa kuma baƙar fuska suna duban Afirka da ita, in ka ji an ce baƙar fuska, ana nufin baƙar zuciya baƙin tunani.
To wasu lokutan musamman wannan shugaban da ya zo, a ɓaramɓarama ana ganin wancan shugaban nasu da wuce ba zai kai shekara huɗu bai jefa ta a yaƙi da wata ƙasar ba, to a nasa tunanin gani yake duniya za ta yi ladab ta bishi yadda yake so, amma ba ya da tunani mai yawa a kan haɗa yaƙe-yaƙe.
To shi kuma da ya zo wannan shugaban Amurka da ya zo na yanzu, za ka ganshi salina alim, amma an daɗe ko Regan da Bush ba ina nufin Bush ƙarami ba, Bush babba da ƙarami ko su ba sa nufin hargitsa duniya kamar wannan.
To Amurka ƙawar Nijeriya ce, kullum muna tunani mai kyau akan Amurka, kuma muna ganin in Allah ya so ya yarda a ƙarshen abubuwa ƙasashen nan guda biyu za su dawo su daidaita su yi maslaha da ƙasashen duniya kada su zama barazana ga ƙasheshen duniya. Da yawansu in sun yi barazanar ma kansu take komawa. Abin da ake nufi da kansu yake komawa, duk da dai Dal aba komai bace a wurin Amurka, amma da aka fara faɗan Yukiren zuwa yanzu ta yi asarar fiye da Dala biliyan 30, irin wannan ƙoƙarin Chana take yi, wurin da wani zai yi asarar biliyan 30 sai ta yi tsarin yadda za ta yi kasuwancin Dala biliyan 30.
Yadda aka taho a haka, inda Amurka ta yi asara ita kuma Chana samun riba take yi, nan gaba idan Amurka ta yi wasa kabunta na riƙe da mulkar duniya zuwa wani lokaci kafin 2030 ina tsoron kada ya faɗi Chana ta ɗauke shi, to amma bama fatan haka, kawai dai fatanmu da su kyakkyawan tunani a kan ƙasashen Afirka da ƙasashen duniya.
Wanne kira ka ke da shi daga ƙarshe?
‘Petriotic Elders Of Nigeria Peace And Justice’ koda wane lokaci suna kiran duniya a zauna lafiya, zama na ƙaunar juna da girmama juna, wannan kawai si ne zai fidda duniya.
Ina kira ga ‘yan Nijeriya Kiristammu da Musulmi babu abin da ya kamata mu yi Nijeriya sai addu’a, A llah ya daidaita ƙasarmu, A’ah ya taimaki shugabanninmu, A’ah ka zaɓa mana shugabannin da za su fitar da mu daga wannan hali, domin Petriotic Elders kullum muna kiran ‘yan Nijeriya da a zauna lafiya, a yi wa shuagabannin da za su zo, sannan a buɗe ido inda ya kamata a taimaka wa jami’an tsaro a taimaka musu.