Gwamnatin jihar Kano ta sanar da dokar hana amfani da injin sare Bishiya ba bisa ka’ida ba a fadin jihar.
Kwamishinan Muhalli da Sauyin yanayi a Jihar Dr. Dahiru Muhammad Hashim ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai ranar Talata a Kano.
- Babu Shirin Gaggawa Wajen Fara Aiwatar Da Harajin Kashi 5 Na Man Fetur – Minista
- Nazarin CGTN: Cin Gajiyar Damarmaki Tare Da Samun Sakamakon Moriyar Juna Ta Hanyar Yin Komai A Bude
Hashim ya ce, matakin ya zama dole domin magance matsalar sare itatuwa a faɗin jihar.
“Wannan matakin ya zama dole don dakatar da saran gandun daji, kare muhalli, da tabbatar da ɗorewar albarkatun ƙasa,” in ji Dokta Hashim.
Ya yi gargaɗin cewa, duk wanda ya karya doka zai fuskanci hukunci mai tsauri. “Za a tsaurara doka, tare da biyan tarar ₦500,000 da kuma yiwuwar ɗauri a gidan yari saboda amfani da injin sare bishiya ba tare da izini ba, da kuma tarar ₦250,000 kan kowace bishiya da aka sare ba bisa ka’ida ba.
“Haka kuma za a umurci waɗanda suka aikata laifin da su sake dasa bishiyar sannan kuma za a ƙwace injin,” in ji shi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp