Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa mai yuwuwa ta sake dawo wa gaban hadakar majalisar kasar don ta nemi amincewar ‘yan majalisar tarayya a kan kara yawan kasafin kudin 2024, amma idan ta samu kari kudaden shiga da ta ayyana za ta samu.
A makonnin da suka gabata ne, Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya gabatar wa majalisar kudurin kasafin kudin 2024, wanda ya kai naira tirliyan 27.5.
- Kwamitin Majalisar Dattawa Ya Nemi A Karawa Ma’aikatar Yaɗa Labarai Kudi Kan Kasafin 2024
- Sin Na Taka Rawar Gani Wajen Raba Fasahohinta Na Bunkasa Tattalin Arziki Na Zamani Da Sauran Kasashe Masu Tasowa
Ministan kudi da tattalin arziki, Mista Wale Edun shi ya bayyana hakan a lokacin da yake kare kasafin kudin a gaban kwamitin majalisa da ke kula da harkokin kudade.
Edun ya kuma shaida wa ‘yan kwamitin cewa, an samu gagarumin ci gaba a fannin tara kudaden shiga na kasar nan a ‘yan watan da suka gabata, inda ya kara da cewa, kudaden shigar na gwamnatin sun karu.
Ya ci gaba da cewa, gwamnatin na yin dubi a kan yadda za ta kara hanzarta kashe kudin da ta ware a cikin kasafin kudin 2024.
A cewar Edun, kudin shigar ya kai kashi biyar a cikin dari, wanda hakan ya nuna wani kwarin gwiwa kan samun kudaden musaya duk da cewa darajar naira ya ragu, sannan akwai sauran bashin da ake bin gwamnatin wanda ya kai kimanin dala 46.
Ya kara da cewa bashin da gwamnatin ta biya ya kai kashi 18 a cikin dari, inda ya kai kasa da abin da aka ware a cikin kasafin kudin na badi.
Ministan ya sanar da cewa gibin da aka samu a kasafin kudin ana sa ran zai ragu daga naira tiriliyan 13.7 zuwa naira tirilyan 9.2.
Ya sanar da cewa, yawan kudin da za a amso bashi a cikin kasafin kudin ya ragu daga kashi 6.1 a cikin dari zuwa kashi 3.9.
Edu ya kara da cewa wannan kasafin kudi ne ta sake sabunta fata wannan kasa shi ya sa mai girma shugaban kasa ya aiwatar da shi cikin lokaci.
A nasa bangaren shugaban kwamtin harkokin kudade, Sanata Sani Musa ya bayyana cewa Nijeriya na cikin wani mawuyacin hali a fannin tattalin arziki, musamman a bangaren rashin aikin yi.
Sai dai, Musa ya ce yana da yakinin cewa, gwamnatin Shugaba Tinubu na kan yin dukkanin mai yuwa don lalubo da mafita a kan wannan kalubalen.