Kungiyar kwadago ta Nijeriya (NLC) ta ce za a iya tattaunawa kan sabon mafi karancin albashi zuwa N100,000 ko N200,000 saboda tsadar rayuwa.
A yayin da kungiyar kwadago da kuma TUC suka shirya fara yajin aikin a ranar Talatar da ta gabata, sakamakon tasirin cire tallafin man fetur, sun ajiye yajin aikin ne bayan wata ganawar da suka yi da hukumomin gwamnati a Abuja da yammacin ranar Litinin.
Sai dai a cewar shugaban kungiyar ta NLC, Joe Ajaero, sun dauki matakin ne domin bai wa gwamnati lokaci domin ta cika wani bangare na yarjejeniyar da aka cimma da kungiyoyin kwadago, inda ya kara da cewa bayar da karin albashin N35,000 – wani bangare na tayin gwamnati – ba sabon abu bane. mafi karancin albashin da ya ce a bai wa ma’aikata zai iya kai wa N200,000.
“Don haka, ba mafi karancin albashi ba ne abun dubawa. Don haka, idan a watan Maris, Afrilu, ko kafin lokacin za mu tattauna kan sabon albashi wanda zai iya zama N100,000 ko N200,000, za a rubuta shi a matsayin dokar mafi karancin albashi wanda ya kamata ya zama doka,” in ji shi a yayin tattaunawa da gidan talabijin na Channels.
Da yake tabbatar da cewa kyautar N35,000 ba kari ba ne a kan mafi karancin albashi na N30,000 na kasar, shugaban NLC ya ce za a yi la’akari da abubuwa da yawa game da sabon albashin.
“Wasu abubuwa za su shigo cikin idan muka tattauna su- hauhawar farashin kayayyaki, tsadar rayuwa. Duk wani abu zai shigo ciki, ”in ji shi.
“Ba za mu je neman N65,000 ba.”
A cewarsa, domin sabon mafi karancin albashi ya fara aiki, majalisar dokokin kasar za ta taka muhimmiyar rawa.
“Mafi karancin albashi ya samo asali ne daga doka. Har sai an kafa shi a Majalisar Dokoki ta kasa, bai zana mafi karancin albashi ba,” Ajaero ya kara da cewa.