Ana iya cimma muradun kulawa da lafiya yadda ake yi sauran kasashen duniya nan da shekara ta 2030, jagoran shiyyar Arewa ta tsakiya na hukumar inshora ta kasa (NHIA,Mista Adelaja Abereoran ne ya bayyana hakan.
Ya bayyana cewar yadda za a gaggauta aiwatar da su tsare- tsare na dokar kafa hukumar tare da hadin kan duk masu ruwa da tsaki,wanda kuma hakan ne zai samar da hanyar cimma su muradun kulawa da lafiya kamar yadda ake yi a kasashen da suka cigaba na da shekara ta 2030.
- Messi Ya Fi Maradona A Argentina –In Ji Kocinsa
- 2023: Atiku Ya Sha Alwashin Ƙara Wa Jihohi Da Ƙananan Hukumomi Ƙarfin Iko
Abereoran ne ya bayyana cewa yanzu tilas ne ga kowanne dan Nijeriya kowanne dan Nijeriya yayi rajista da tsarin inshorar lafiya ta kasa, lokacin da yake ganawa da ‘yan jarida a Ilori hedikwatar Jihar ranar Juma’a.
Ya kara jaddada cewar: “NHIA tana yin gyara a hukumar domin ta aiwatar da ayyukanta na cimma muradun lafiya ga ‘yan Nijeriya kamar yadda ake yi a sauran kasashen da suka cigaba nan da shekara ta dace nan da shekara ta 2030.Wannan kuma an dogara ne ko samun wata madafa na muradan cigaba.”
Abereoran shi ne yake kula da Jihohin Kwara,Kogi da kuma Neja,ya bayyana wadansu daga cikin gyare- gyaren da ake son kawowa da suka hada da wayar da kan al’umma, tabbatar da tsage gaskiya da aiwatar da ita,da taimakawa kokarin da ke yi na cimma muradun kulawa da lafiyar al’umma kamar yadda ake yi a kasashen dasuka cigaba.Wadannan muradun za a iya cimma su ta hanyar kara inganta tsare- tsaren kulawa da lafiyar al’umma wadanda ake yi a halin yanzu.
Ya bayyana dokar inshorar lafiya ta kasa ta shekara Shugaban kasa ne Muhammadu Buhari ne ya sa mata hannu akanta ranar 19 ga watan Mayu,2022 wata doka ce da zata inganta harkar kula da lafiyar ‘yan Nijeriya.
Darektan shiyyar ya kara bayani inda yace,“ wasu daga cikin matakan da aka dauka suna taimakawa warai da gaske.
Hukmar inshorar lafiya ta kasa ta samu karramawa saboda matakani da kawo daukin da tayi.Daga cikinsu akwai saboda bin matakan fasahar zamani IT wanda NITDA ta bata.Watti duk hukumomi; sahun farko daga SERBICOM;sai kuma bin dokoki, da nuna gaskiya (EICS 2022) inda ta samu kashi 74.5 daga ICPC.”
Abereoran yayi kira kungiyar ‘yan Jarida ta kasa reshen Jihar Kwara (NUJ) ta hadakai da hukumar inshorar lafiya ta kasa domin wayar da kan al’umma,inda har ya saima ‘yan jaridar inshorar ta shigar da su cikin tsarin a matsayinsu na kungiya.
Da yake fadar albarkacin bakinsa shugaban kungiyar ‘yan jarida na Jihar Kwara na Jihar Kwara, AbdulLateef Ahmed,ya godewa Shugabannin hukumar saboda yadda suke tafiya tare da ‘yan jarida wajen aiwatar da tsare- tsarensu a Jihar.