Ƙungiyar Al Hilal da ke Saudiyya ta amince da biyan Yuro miliyan 53 domin siyan ɗan wasan gaba Darwin Nunez daga Liverpool.
Nunez, mai shekara 26 daga Uruguay, ya koma Liverpool daga Benfica a shekara ta 2022 a kan fam miliyan 64.
- Masu Ƙwacen Waya Sun Kashe Ɗalibin BUK A Kano
- Jami’an Tsaro Sun Daƙile Harin ‘Yan Bindiga A Zamfara, Sun Ƙwato Bindigogi
Yanzu yana shirin zuwa Al Hilal bayan an kammala yarjejeniya, kuma za a duba lafiyarsa kafin ya kammala komawarsa.
Tun da ya zo Liverpool, Nunez ya ci ƙwallaye 40 a wasanni 143.
Amma a kakar da ta gabata, wasanni takwas kacal aka fara da shi a gasar Firimiyar Ingila.
Sayar da Nunez zai ba Liverpool damar siyan Alexander Isak daga Newcastle.
Sai dai Newcastle ta ƙi karɓar tayin fam miliyan 110 daga Liverpool, saboda tana so ta siyar da Isak ne abkan fam miliyan 150.
Liverpool ta riga ta siyo Florian Wirtz daga Bayer Leverkusen a kan fam miliyan 116 da kuma Hugo Ekitike daga Frankfurt a kan fam miliyan 79.
Hakan ya sa Liverpool ta kashe kusan fam miliyan 250 a wannan kakar kasuwanni.
Ta kuma siyar da Luis Diaz ga Bayern Munich ankan fam miliyan 65.5 da Tyler Morton ga Lyon a kan fam miliyan 15.
Ɗan wasan Ingila Harvey Elliott ma na iya barin ƙungiyar a bana.
A watan Janairu da ya wuce, Liverpool ta ƙi karɓar tayin Yuro miliyan 70 daga Al-Nassr domin siyan Nunez.
A kakar da ta gabata, Nunez ya ci ƙwallaye bakwai ne kacal, amma a watan Yuli ya ci ƙwallaye uku cikin minti 20 a wasan da suka buga da Stoke City.
Al Hilal, wadda Simone Inzaghi ke jagoranta, ta zo ta biyu a gasar Saudi Pro League a bara.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp