Yanzu haka, an shiga lokacin bazara a nan kasar Sin. Tun can baya da kuma yanzu, al’ummar kasar Sin na jin dadin kallon furanni a lokacin bazara, lokacin da furanni iri daban daban suka fito bayan dogon lokacin hunturu mai sanyi. Alal misali, yin wasa da kayan goge na gargajiyar kasar Sin da dafa shayi a cikin bishiyoyin Peach, kallon taurari da dare tsakanin bishiyoyin Cherry blossom, da daukar hotunan masu sanye da tufafin gargajiyar kasar Sin cikin gonakin furannin Rape.
Mutanen da ke zama a sassa daban daban a kasar Sin suna ta ziyarar bude ido don kallon kyawawan furanni a lokacin bazara. Yau za mu yada zango a wani gidan ibada da ke birnin Beijing don kara sanin yadda mazauna wurin suke jin dadin kallon furannin Magnolia.
- Wang Yi Da Qin Gang Sun Gana Da Ministar Harkokin Wajen Jamus
- Sin Na Adawa Da Matakin Amurka Na Sanya Kamfanonin Kasar Cikin Jerin Sunayen Kamfanonin Da Ta Sanya Musu Takunkumi
Shaharren gidan ibada na Dajuesi mai tsawon tarihin shekaru kusan dubu daya da ke babban tsaunin Xishan na birnin Beijing, hedkwatar kasar Sin, cike yake da kamshin furannin Magnolia a Sinanci a lokacin bazara. Mazauna wurin masu dimbin yawa suna da al’adar jin dadin kallon furannin na Magnolia dake gidan ibada na Dajuesi a lokacin bazara tun da can, har ma lamarin da ya zama al’ada ga wasu daga cikinsu a ko wace shekara. A yayin da furannin Magnolia suka fara nunawa a lokacin bazara na shekarar da muke ciki, an bude shagalin furannin Magnolia a wurin shan shayi na Minghui a gidan ibada na Dajuesi, wanda a kan shirya a ko wace shekara.
An fara gina gidan ibada na Dajuesi ne a shekara ta 1068 bayan haihuwar Annabi Isa A.S., wato a zamanin daular Liao ta kasar Sin. Sakamakon kasancewar wani rafi da ya ratsa wannan gidan ibada, ya sa gidan ibadan na da suna na daban wato gidan ibada na Qingshuisi. Abun da ya fi shahara a gidan ibada na Dajuesi shi ne itacen Magnolia mai tarihin shekaru fiye da dari 3.
Sun Rongfen, darektar ofishin kula da harkokin gidan ibada na Dajuesi ta yi mana karin bayani da cewa, “Yanzu lokaci ne da itatuwan Magnolia suke fid da furanni. A yayin da muke shirya shagalin jin dadin kallon furannin Magnolia, mun kuma shirya wani shagalin nune-nune da sayar da littattafan hotunan furannin. Mutane na iya ziyartar shagalin, tare da kallon furannin, shan shayi, kallon yadda ake soya ganyayen shayi, da sauraren kide-kiden addinin Buddha. Gidan ibadan Dajuesi yana samar da jin dadi da nishadi da kuma hutawa sosai.”
Furannin Magnolia, alama ce ta gidan ibada na Dajuesi, haka kuma abu ne mai kyaun gani a wajen. Shagalin baje kolin al’adun furannin Magnolia da a kan yi a kowane lokacin bazara a gidan ibada na Dajuesi ya samu karbuwa sosai.
Xuan Lipin, mai kula da harkokin gidan ibada na Dajuesi ta gaya mana cewa, “Tsawon tarihin icen Magnolia da ke gidan ibadanmu na Dajuesi ya wuce shekaru dari 3. Shi ne icen Magnolia mafi tsufa a nan birnin Beijing. Hakan shi ke nuna alamar gidan ibada na Dajuesi. Ya kan kuma fid da furanni misalin ran 5 ga watan Afrilu a kowace shekara. Saboda ya tsufa sosai, shi ya sa ya kan fid da manyan furannin da girman kowanensu ya yi daidai da hannun mutum. Furannin suna da kyan gani sosai. A lokacin zafi na kowace shekara, icen kan yi toho. A cikin lokacin hunturu mai sanyi, a yayin da dukkan ganyayen itatuwa suka fadi, tohon bai mutuwa. A lokacin bazara dake tafe kuwa, icen ya kan fid da furanni. Sakamakon jure wahalar tsananin sanyi ya sa fararen furannin Magnolia suke da matukar kyaun gani.”
A kowane lokacin bazara, icen Magnolia da ke gidan ibada na Dajuesi kan fid da manyan furanni tare da samar da kamshi mai dadi. A duk lokacin da fararen furannin suke nunawa, dimbin matafiya kan kawo ziyara. Kyaun surar furannin Magnolia da ke gidan ibada na Dajuesi da kuma kamshinsu da siffofinsu babu kamarsa a nan Beijing.
Baya ga jin dadin kallon furannin Magnolia, matafiya suna shan shayi cikin kwanciyar hankali a gidan ibada na Dajuesi.
Madam Murong Zigui, babbar darektar wurin shan shayi na Minghui da ke wannan gidan ibada ta gaya mana cewa, ruwan rafin da ya ratsa ta gidan ibada na Dajuesi yana taimakawa sosai wajen dafa shayi, inda ta ce, “Ruwan da ake amfani da shi wajen dafa ganyayen shayi na da matukar muhimmanci, in babu ruwan da ya dace, to, ba za a iya dafa ganyayen shayi yadda ya kamata ba. A cikin irin wannan wuri mai matukar ni’ima, da kuma rafin da ya ratsa ta gidan ibadan mai tarihin shekaru dubu daya, wanda ake iya shan shayi, tare da morewa da kallon kyaun surar muhallin halittu da kuma sauraren kukan tsuntsaye da safe, da shakar kamshin furannin Magnolia. Shayi, ruwa da ni’itattun wurare dukkansu na da kyau sosai.”
Haka batun yake, kamshin shayi da na furannin na Magnolia da kuma itatuwa masu dogon tarihi su ne sigogin musamman na gdian ibada na Dajuesi.
Gidan ibadan Dajuesi mai tarihin shekaru dubu daya, icen Magnolia mai tarihin shekaru dari 4 da kamshin shayi mai dadi sun taimakawa mutane, kaucewa hayaniyar birane, sun kuma samarwa mutane kwanciyar hankali, tare da mantawa da gida.
A yayin shagalin nune-nunen al’adun shayi da tunanin Buddha da aka yi a gidan ibada na Dajuesi, Yan Zang, dan Buddha kwararre a ilmin addinin Buddha kuma mashawarci na gidan ibada na Dajuesi a fannin ilmin addinin Buddha ya yi mana karin haske kan ma’anar shan shayi a wajen ’yan addinin Buddha, inda ya ce, “A matsayinsa na wani bangare na zaman rayuwarmu ’yan addinin Buddha, shan shayi ya kasance tamkar abu ne na tilas gare su wajen kyautata jiki da kuma tunani. A lokacin da muke shan shayi, kamata ya yi mu tuna da abubuwa da dama. Da farko, ganyayen shayi ba sa girma, sai bayan shekara guda, sa’an nan in ba a yi aiki tukuru ba, to, ba za a yi girbin ganyayen shayi masu kyau ba. Ga karamin kwaf daya na shayi, ruwan da dafa shi ya fito ne daga muhallin halittu, yayin da ganyayen shayin sun girma ne sakamakon hasken rana. Don haka tilas ne mu gode wa muhalli, al’umma baki daya. Na biyu kuma, ya kamata mu sha shayi tare. Ko da yake shayi na da kyau, amma idan mutum ya sha shayi shi kadai, to, ba zai ji dadinsa ba. In muka sha shayi tare da abokai da dama, to, za mu kara jin dadi. Na uku, kar mu damu da abubuwan da muka samu da muka rasa. Kafin mu yi barci, mu kan waiwayi abubuwan da suka abku a ranar, mu kan ji dadi idan muka yi sabbin abokai, ziyartar wasu sabbin wurare da samun abubuwa masu nagarta, amma a daidai wannan lokaci, bai dace mu nuna damuwa kan abubuwan da muka samu ko abubuwan da muka rasa, saboda gobe ma rana ce. Wannan ya sa ake cewa, shan shayi na iya kyautata halayyar mutm, da kuma karfafa kauna a tsakanin mutane, haka kuma, gidan ibada na Dajuesi, wuri ne da ke iya kyautata halayyar mutane da karfafa kauna a tsakanin mutane.”
A lokacin bazara da furanni suke nunawa, matafiya na ta zuwa gidan ibada na Dajuesi domin kara fahimtar sigar musamman na wurin.
Madam Wang Jing da ke ziyara a gidan ibada na Dajuesi ta gaya mana cewa, “Wasu abokaina sun fada min cewa, gidan ibada na Dajuesi ya dace da ziyara. Yana kusa da gida na. Mintoci fiye da 10 ne kawai daga gidanmu zuwa nan a mota. Akwai iska mai ni’ima da itatuwa masu dogon tarihi. Muhallin wurin ya sha bamban da na birni. Mun zo nan ne tare da yaronmu, ta yadda zai iya morewa da kallon furanni da shakar iska mai kyau da ziyartar gine-ginen gargajiya.”
Gidan ibada na Dajuesi da ke babban tsaunin Xishan na Beijing, mai tsawon dubban shekaru, yana ci gaba da bayyana kyan surarsa sosai, tare da jawo dimbin matafiya daga sassa daban daban.
Ba Aimin, mataimakin shugaban hukumar harkokin abubuwan tarihi ta birnin Beijing ya yi bayani da cewa, ni’imtattun wurare da al’adun gargajiya dake gidan ibada na Dajuesi, su ne ainihin sigar musamman da ke jawo hankalin mutane. Yana mai cewar, “Nan gaba za mu kyautata gidan ibada na Dajuesi ta fuskar al’adu da yanayin gargajiya. Akwai tsauni da ruwa da shayi a nan, wannan zai kara kyautata tunaninmu.” (Mai fassarawa: Tasallah Yuan daga CMG Hausa).