Afirka na daya daga cikin nahiyoyin da aka yi wa shaida da rikon al’adu na gargajiya da aka gada tun iyaye da kakanni. Watakila shi ya sa har yanzu mutanen yankin suke rike da wasu al’adunsu da ake kallon za su iya bacewa saboda sauye-sauyen zamani da ci gaban wayewar kai da kuma dunkulewar duniya a wuri guda, sai dai hakan ba ta faru ba.
Yayin da wasu al’adu na indiya ke da ban sha’awa kamar bukukuwan bikini Holi ko fasa kwakwa, haka nan wasu al’adun Afirka na da nasu birgewar musamman ga masu yi. Duk da rashin fahimtar da wasu za su nuna, wadannan al’adun suna da ban mamaki da al’ummomin Afirka ke yi wanda ko da kudi aka ce wand aba dan gado ba ya aikata, zai ce a kai kasuwa.
- Noman Aya Da Yadda Yake Samar Da Kudin Shiga
- Bunkasuwar Tattalin Arzikin Sin Ya Kara Imanin Sassan Kasa Da Kasa Game Da Kasar
Bambance Bambancen Afirka:
Afirka, wacce take nahiya ta biyu mafi girma a fadin duniya na alfahari da tarin al’adun gargajiya da aka bayyana ta nau’i daban-daban kamar raye-raye, kida, zane-zane da kayan kwalliya.
Ga jerin kabilu da wasu al’adun da suke yi masu ban al’ajabi.
Tofin Yawu na Kabilar Maasai
Mutanen maasai, mazauna Arewacin Tanzaniya da Kenya, na matukar kiyaye al’adunsu wadanda ke da muhimmanci ga asalinsu maimakon arowa daga wani wuri. Daya daga cikin al’adun ya hada da tofin yawu a hannu a matsayin nuna girmamawa, sukan yi tofi a hannunsu a domin nuna girmamawa da albarka ga baki ko daidaikun mutane da suke wa lale marhabin. Matasan kabilar maasai, sukan yi tofi a hannun kafin su gaishe da dattawa ko kuma yin musabaha da hannu, wanda ke nuna gaggarumar girmamawa ga junansu.
Kaciyar Matan A Kabilar Mursi Da Ke Habasha
A kabilar Mursi na kasar Habasha, ana gudanar da wata al’ada ta ‘yan mata inda wata dattijuwa ke yi wa ‘yan mata kaciya ta hanyar yanke wata fata a cikin farji, da zarar yarinya ta kai shekaru goma sha biyar 15 da haihuwa. Bayan an yanke za a bar raunin ya warke tare da amfani da yumbu. Haka nan suna da wata al’ada ta Sanya farantan katako a tsakanin lebban mace, yawanci an fi zaben wannan al’ada ta farantin lebe, musamman a lokacin budurtaka.
Tsallen Bajimin Sa a Kabilar Hamar
A kasar Habasha, kabilar Hamar sun shahara da dukiyar dabbobi, suna gudanar da wani biki mai tsananin bukatar koyon atisaye da jiki wanda aka fi sani da tsallen bajimi. A ka’idar al’adar, samari kan shafe kwana uku suna bukukuwan tsayawa a kan bajimi suna dirowa yayin da shi kuma bajimin ke gudu sosai. Bikin na nuna mutunci da jaruntaka.
Al’adar Sace Mace A wodaabe
Wata al’ada mai ban al’ajabi ita ce ta Kabilar Wodaabe da ke kasar Nijar inda aka amince da sace mace. Samari tun suna kanana ake masu mata, sannan akan yi neman matar da za a aura a wani bikin da suke gudanarwa shekara-shekara. Idan saurayi ya yi nasarar sace mace ba tare da an gane ba a wannan bikin to saurayin wanda shi ne zai zama mijinta zai samu daukaka ko matsayi mai girma a cikin al’ummar.
Takaba A Kabilar Inyamurai A Nijeriya:
A yankin Inyamurai (Igbo) a Nijeriya, masu takaba kan yi jimamin rasuwar mazansu, ta yadda suke kokarin nuna zahirin bakin cikin da suke ciki. A irin wannan zaman makoki, dole ne sanya bakaken kaya don kawar da munanan al’amura daga iyalin da aka yi wa mutuwa.
Bikin Matattu na Kabilar Chewa
A kabilar Chewa da ke kasar Malawi, ana gudanar da bikin tsarkake ‘yan kabilar da suka rasu, wanda ya hada da yanke wani sashi na gawa a bude ta, kana a zuba ruwa ta cikinta. Sannan a yi amfani da ruwan da aka tsarkake gawar da wajen shirya liyafa ta gama gari.
Al’adar Sharo ta Fulani
A kabilar Fulani na Nijeriya, ana yin wata al’ada da ake kira sharo, wanda a yayin gudanar da ita akan yi wa saurayi duka mai tsanani da babbar bulala ta danyen ice don a gwada jarumtarsa ta aure. Idan ya iya jure dukan, za a ci gaba da shirye-shiryen aurensa, idan ya kasa jurewa, za a fasa tare da kin biyan sa duk abin da ya yi wa yarinyar hidima.
Gwajin Amare
Akwai wata karamar kabila da ke kasar Yuganda, da take da al’adar dole ne ango ya kwaikwayi yin wani abinci da suke soyawa irin wadda Innar amarya ta shirya don tantance ko da gaske ya shirya yin aure ko a’a. Bugu da kari, innar amaryar kan duba budurcin amaryar kafin ta tare domin tabbatar da cewa an ba shi ‘ya mai cike da koshin lafiya.