Abokai, yau na zana wani Cartoon dangane da bikin Duanwu na kasar Sin, bikin gargajiya da ke da tsawon tarihi na sama da shekaru 2000. Ban da manufofin da Sin ke da su game da kare al’adun gargajiya, yadda al’ummun Sinawa suke amincewa tare da alfahari matuka da al’adunsu, ya sa bikin ya dore har tsawon shekaru sama da 2000, har ma duniya ta san da shi yanzu.
Zongzi nau’in abincin gargajiya ne da ba a iya rasa shi ba a yayin bikin, kuma na san akwai wani abinci da ake kira Tubani a Nijeriya, wanda kusan iri daya ne da Zongzi da ake dafawa a lokacin bikin Duanwu.
Ina tsamanin cewa Tubani ma na alamta al’adun Hausa. Ku ba ni bayanin tarihin Tubani. (Mai zane: Amina Xu)